Tofa: Mutane 2 Sun Mutu Ana tsaka da Daukar Shirin Sabon Fim a Najeriya

Tofa: Mutane 2 Sun Mutu Ana tsaka da Daukar Shirin Sabon Fim a Najeriya

  • Rundunar yan sandan Legas ta fara binciken mutuwar ma'aikata biyu da aka tsinci gawarsu ana tsaka da daukar shirin fim
  • An ce Ekemini Imeh da Ayodeji Odediran sun mutu ne yayin da suke hutawa a cikin mota bayan sun gama girka kaya haske
  • Zuwa yanzu an fara gwaje-gwaje kan gawarwarkin ma'aikatan, bayan an ga kumfa a bakunansu da kuma jini a hanci da lebe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wasu mambobi biyu na rukunin masu shirya fina-finai na Nollywood a Lekki.

An tsinci gawarwakin ma'aikatan ne a cikin wata mota da aka ajiye a wurin da ake ɗaukar fim, inda aka gano ba sa numfashi a ranar Asabar, 7 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gidan limamin masallacin Izala da dare, sun sace iyalansa

An tsinci gawar ma'aikatan Nollywood 2 a wajen daukar fim
Wasu ma'aikata na daukar shirin fim. Hoto: ISSOUF SANOGO / Getty Images. A kula: Mutanen da ke cikin hoton ba su da alaka da labarin, an sanya don misali ne kawai.
Source: Getty Images

Abin da ya faru a wajen daukar fim

Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da shugaban sashen haske, Ekemini “GeeTee” Imeh, da abokin aikinsa, Ayodeji Walter Odediran, in ji rahoton jaridar Punch.

Wata majiyar ƴan sanda ta bayyana cewa Imeh da Odediran sun isa wurin ɗaukar fim ɗin ne da tun da duku duku domin girka kayan aikin haske.

Bayan sun kammala aikin su, sai suka shiga cikin wata mota samfurin Nissan mai baƙin gilashi da aka ajiye a wurin domin su huta.

Wani jami'in dan sanda da ya nemi a saka sunansa ya ce:

"Ma'aikatan biyu sun gama girka kayan wuta tun kafin a fara daukar shirin fim din da Boma na Big Brother ya jagoranta.
"Da misalin karfe 11:00 na safe, an kai musu karin kumallo cikin motar yayin da na'urar hura sanyi (AC) ke kunne."

Ma'aikata a Nollywood sun mutu a mota

An fara shiga damuwa ne lokacin da aka riƙa kiran wayoyinsu amma ba sa ɗagawa, yayin da ake tsaka da gudanar da ayyukan ɗaukar fim din.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai wasikar kai hari kauyuka, mutane sun fara gudu

Majiyar ta kara da cewa:

"Sai bayan da aka gama daukar fim din da karfe 8:00 na dare aka gano gawarwakinsu a cikin motar da suke ciki."

Majiyar ta ƙara da cewa an tsinci mutanen suna fitar da kumfa a baki, yayin da ɗayan ke fitar da jini a kewayen hancinsa da kuma laɓɓansa.

Wata majiyar ƴan sandan ta bayyana cewa an riga an kai rahoton lamarin zuwa ofishin ƴan sanda na Maroko dake jihar Legas domin gudanar da bincike.

Rundunar 'yan sanda ta ce ta fara bincike don gano abin da ya kashe ma'aikatan fim
Wasu ma'aikata da ke aikin daukar fim. Hoto: ISSOUF SANOGO / Getty Images. A kula: Mutanen da ke cikin hoton ba su da alaka da labarin, an sanya don misali ne kawai.
Source: Getty Images

Matakin da hukumomi suka dauka

A halin yanzu, ana duba faya fayan bidiyo na CCTV na wurin da abin ya faru, sannan an kai gawarwakin dakin ijiye gawarwaki na asibiti, in ji rahoton This Day.

Kakakin yan sandan Legas, Abimbola Adebisi ya ce:

"An mayar da maganar zuwa sashen binciken manyan laifuffuka dake Panti, Yaba domin ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi.
"An kuma fara gudanar da gwajin gawa, musamman bangaren gano sinadaran guba domin tantance ainihin abin da ya yi sanadiyar mutuwar wadannan kwararrun ma'aikatan fim."

Kara karanta wannan

Lamari ya juya: Ƴan bindiga sun yi saɗaf saɗaf sun hallaka 'DPO' bayan sace shanu

Imeh, kafin rasuwarsa, shi ne babban jami'in wani kamfanin haske kuma ya yi ayyuka a manyan fina-finai kamar King of Boys da bidiyon Davido.

Jarumar Nollywood ta mutu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an tabbatar da rasuwar fitacciyar jaruma kuma mai shirya fina-finai a Kudancin Najeriya, Allwell Ademola.

Jarumar ta rasu tana da shekaru 43 awa 24 bayan ta sake bidiyo cewa sai taga karshen shekarar 2025; sai dai ta mutu din ne a ranar 27 ga Disamba, 2025.

Mutuwarta ta jefa masoya da abokan aikinta a cikin tsananin alhini, inda fitattun jarumai da ma'aikatan Nolyywood suka aika sakon ta'aziyyarsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com