Tijjani Gandu Ya Yi wa Kwankwaso Sabuwar Waka Abba na Fita daga NNPP

Tijjani Gandu Ya Yi wa Kwankwaso Sabuwar Waka Abba na Fita daga NNPP

  • Mawakin Kwankwasiyya, Tijjani Gandu, ya fitar da gajeriyar waka da ke nuna goyon bayansa ga Rabiu Musa Kwankwaso tare da nisantar Abba Kabir Yusuf
  • Wakar ta biyo bayan sanarwar ficewar Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP, lamarin da ya sake tayar da muhawara a siyasar Kano
  • Dubban mutane sun mayar da martani kan wakar, inda magoya baya suka bayyana ra’ayoyi masu nuna goyon baya da addu’o’i ga mawakin tafiyar Kwankwasiyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Mawakin Kwankwasiyya, Tijjani Hussaini wanda aka fi sani da Tijjani Gandu, ya saki wata gajeriyar waka da ke bayyana matsayarsa a rikicin siyasar Kano da ya biyo bayan ficewar Abba Kabir Yusuf daga NNPP.

Tijjani Gandu ya bayyana goyon bayansa ga jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da ya nesanta kansa daga Abba Kabir Yusuf, wanda ya sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma’a, 23, Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Me ya rage wa siyasar Kwankwaso bayan ficewar Abba? An sama masa mafita

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Tijjani Gandu
Mawakin Kwankwasiyya, Tijjani Gandu da Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Tijjani Hussaini
Source: Facebook

Bidiyon da mawakin ya fitar a Facebook ya kara jawo hankalin jama’a, musamman a shafukan sada zumunta, inda ake ta bayyana ra’ayoyi mabambanta kan abin da ya faru da kuma tasirinsa ga siyasar Kano.

Sakon Tijjani Gandu da wakarsa

Yayin sakin wakar, Tijjani Gandu ya wallafa wani sako a shafinsa, inda ya jaddada kudirinsa na yin waka da magana ba tare da karya ko wuce ka’ida ba. A cikin sakon, ya ce zai yi waka, zai yi magana kuma zai yi rubutu ne cikin gaskiya da rikon amana.

Mawakin ya wallafa sakon ne jim kadan bayan ya sanya hotonsa tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, abin da ya nuna a fili inda ya dosa a wannan rikici na siyasa.

Wakar Tijjani Gandu ga Kwankwaso

A cikin wakar da ya saki, Tijjani Gandu ya fito tare da wata ‘yar amshi, inda kalmomin wakar suka mayar da hankali kan nisantar hayaniya, rigingimu da sabani.

Kara karanta wannan

2027: Ana so Kwankwaso ya hada kai da Barau su kifar da Abba a Kano

Wakar ta bayyana cewa shi da mabiyansa ba sa cikin rikice-rikicen siyasa da hayaniyar da ke yawo a wannan lokaci a jihar Kano.

Ga abin da wakar ta kunsa:

"Jagawlgwalan bana, damalmalan bana, cakwal-kwalin bana babu mu.
'Hayaniyar bana, cuku-cukun bana, tiri-tirin bana banda mu.
'Maganganun bana, rigingimun bana, fiitintinun bana babu mu.
'Maganganun bana, kacaniyar bana, rufa-rufar bana banda mu.
"Duka babu mu."

Martanin jama’a kan wakar Tijjani Gandu

Bayan fitowar wakar, jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu. Wasu sun yi addu’a ga Tijjani Gandu, suna masa fatan alheri da samun dacewa.

Wasu kuma sun bayyana cewa sun samu nutsuwa da kwarin gwiwa daga wakar, suna ganin mawakin a matsayin mutum mai rikon amana da gaskiya.

A halin yanzu, Abba Kabir Yusuf da wasu daga cikin hadimansa na ci gaba da ficewa daga NNPP. Duk da haka, har yanzu ba a bayyana jam’iyyar da za su koma ba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da daliban Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

Maganar da Kwankwaso ya yi a Kano

A wani labarin, kun ji cewa jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa ya fito ya yi magana kan halin da ake ciki a siyasar jihar Kano.

Kara karanta wannan

Abba ya rike akidar Kwankwasiyya gam duk da rabuwar da jam'iyyar NNPP

Rabiu Kwankwaso ya gargadi 'yan siyasa da mutanen Kano kan bin kudi maimakon akida, yana cewa da haka ake, da shi ma an saye shi tuni.

Ya yi magana ne a gidansa da ke Kano jim kadan bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da fitarsa daga jam'iyyar NNPP da Kwankwaso ke jagoranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng