Babu Su Gwanja da Aka Saki Sunayen Mawakan Najeriya da Ake Gayyata Manyan Taruka

Babu Su Gwanja da Aka Saki Sunayen Mawakan Najeriya da Ake Gayyata Manyan Taruka

  • Akwai fitattun mawakan Najeriya da suka rera wakokinsu a manyan tarurruka na duniya, inda suka fi tallata kidan Afrobeat
  • Mawakan da suka hada da Davido, Rema, sun amsa gayyatar nuna bajintarsu ne a manyan tarurrukan FIFA, UEFA da AFCON
  • Sai dai kuma, babu wani mawakin Hausa daga da ya taba samun irin wannan gayyata, duk da muna da irinsu Umar M Shareef

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A tsawon shekaru, mawakan Najeriya da dama sun taka rawa wajen kai kiɗan Afrobeats zuwa manyan wurare da fiilayen wasanni na duniya.

Daga gasar cin kofin duniya ta FIFA zuwa UEFA Champions, Ballon d’Or da AFCON, wadannan mawaka sun nuna karfin tasirin salon kiɗan Najeriya a idon duniya.

Jerin mawakan Najeriya da suka halarci manyan tarurruka suka yi wasa.
Mawaki Davido, Rema, Burna Boy na daga cikin mawakan Najeriya da suka yi wasani a manyan tarukan dukiya. Hoto: @heisrema, @davido, @burnaboy
Source: Instagram

Fitattun mawaka a manyan wasanni

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, tauraruwar mawaki Davido ta haska a bikin rufe gasar kofin duniya na 2022 a Qatar, inda ya rera wakar “Hayya Hayya (Better Together)”, daya daga cikin wakokin gasar.

Kara karanta wannan

Tattaunawar Buhari da Lai Mohammed a kan toshe amfani da Twitter a Najeriya a 2021

Burna Boy kuma ya zama tauraron babban bikin bude wasan karshe na UEFA Champions a 2023, abin da ya ja hankalin miliyoyin masu kallo.

Rema ya shiga tarihi a 2023 bayan ya yi waka a bikin Ballon d’Or, inda ya kasance daga cikin ‘yan Afirka kalilan da suka taba yin hakan.

Ita kuwa mawakiya Tems ta kara nuna kwarewarta a duniya bayan rawar da ta taka a wasan rabin lokaci na gasar cin kofin duniya na 2025.

AFCON da rawar da mawakan Afrika ke takawa

A nahiyar Afirka, mawakiya Yemi Alade ta nishadantar da masoya a AFCON 2024, inda ta nuna tsantsar al’adu da kiɗan Afrika.

A hannu daya, Femi Kuti ma ya taba wakiltar Najeriya a bikin bude gasar cin kofin duniya na 2010 a Afirka ta Kudu, inda ya baje kofin kidan Afrobeat ga masu kallo a duniya.

Sauran mawakan Najeriya irin su D’banj, Kizz Daniel, Patoranking, Wizkid da Fireboy DML sun amsa gayyatar yin wasa a manyan tarurruka na kasa da kasa, ciki har da makon NBA All-Star da manyan bukukuwan karrama 'yan wasanni.

Kara karanta wannan

Ahmed Musa ya kawo karshen bugawa Najeriya kwallo bayan kafa tarihi

Davido zai hasa a bikin bude AFCON 2025

A wani sabon ci gaba, Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta sanar da Davido a matsayin babban mawaki a bikin bude gasar AFCON 2025 da za a gudanar a Rabat, Morocco.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa mawaki Davido zai yi waka tare da taurarin duniya irin su French Montana, Douaa Lahyaoui, Lartiste da Says’z.

An shirya bikin ne a ranar Asabar, 20 ga Disamba, a Olm Souissi Fan Zone, daga karfe 6:00 na yamma zuwa tsakar dare, gabanin wasan bude gasar tsakanin Morocco da Comoros a filin wasa na Prince Moulay Abdellah.

Babu mawakan Arewa a wannan jeri

Arewa muna da fitattun mawaka irinsu Ado Gwanja, amma ba a taba gayyatarsu manyan tarurruka na duniya ba.
Fitaccen mawakin Arewa, Ado Ganja yana daukar bidiyon sabuwar waka. Hoto: Ado Gwanja
Source: Facebook

Duk da yadda ake ganin mawakan Najeriya na gabatar da wasanni a manyan tarurruka na duniya, ba a taba ganin an gayyaci wani mawaki daga Arewacin Najeriya ba.

A Arewa, akwai mawaka da dama da suka yi shuhura, wadanda ake sauraron wakokinsu a Najeriya da kasashen da ke jin harshen Hausa.

Kara karanta wannan

Yadda Mikel Obi ya kira Buhari da kansa game da alawus a gasar kofin duniya

Har yanzu dai, mawaka irin su Umar M Shareef, Ado Gwanja, Ali Jita, Nazifi Asnanic, Hamisu Breaker, D.J AB, B.O.C Madaki, Morel, Dauda Kahutu Rarara, da sauransu, ba su taba halartar ire-iren wadannan manyan tarurrukan ba.

Mawaka 10 mafi arziki a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Najeriya na da tarin mawakan da ake ji da su a duniya, kuma wadanda suka mallaki gidaje, motoci, jiragen sama da duk wani alatu.

A Arewacin kasar, dole ne a saka sunan Dauda Kahutu Rarara, Nazifi Asnanic, Ali Jita, Ado Gwanja, Hamisu Breaker, Umar M Sharif, Lilin Baba, a jerin mawaka masu kudi.

Sai dai duk da hakan, an nemi sunayensu an rasa a yayin da aka fitar da jadawalin mawaka 10 mafi arziki a Nigeria, wadanda duk 'yan Kudu ne, da suka hada da P-Square.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com