‘A Ido na Yake Lalata da Mata’: Jarumar Fina Finai Ta Koka kan Halin Mijinta
- Fitacciyar jarumar Nollywood, Mama Ereko, ta bayyana wahalhalun da ta sha a aurenta, ta ce mijinta na kawo mata mata gida a gabanta
- Ta bayyana cewa ta yanke shawarar kin yin aure bayan mutuwar mijinta inda ta fi mayar da hankali kan 'ya'yanta da kiyaye kyan fatarta
- Mama Ereko ta ce ta sha wahala a masana'antar fim, inda masu sayar da fina-finai suka hana ta riba har sai da ta hadu da AbdulRazaq
- Ta ce bata fuskanci cin hanci don samun rawa a fina-finai ba, ta kuma shawarci matasa su fara yin fina-finai da kansu ba tare da bata lokaci ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Fitacciyar jarumar Nollywood, Morenike Sulaimon, wacce aka fi sani da Mama Ereko, ta bayyana wahalhalun da ta fuskanta a aurenta da mijinta marigayi.
Mama Ereko ta fara fim a 1982, amma ta dakata kafin ta dawo a 1994, tun daga lokacin, ta fito a fina-finai da dama, ciki har da Ebun da Ajulo.

Asali: Facebook
Jarumar fim ta fadi matsalolin aurenta
A wata hira da aka wallafa a YouTube, jarumar mai shekaru 79 ta ce 'ya'yanta suna kanana lokacin da mahaifinsu ya rasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jarumar ta ce ta sha wahala sosai a rayuwar aurenta wanda mijinta ke zuwa da mata har cikoin gidanta.
Mama Ereko ta ce:
“Ya kan aikeni yawon hidima idan yana shirin kawo wata mace, Idan na dawo, sai in tarar da wata a gida, amma na gode wa Allah.”
"Dayar budurwar tasa ta fi tsaurin ido, Har tana kwana a gidana, Nakan ji haushi, amma ban isa in ce komai ba, saboda tsoron mijina."

Asali: Instagram
Dalilin jaruma Ereko na kin yin aure
Bayan mutuwar mijinta, Mama Ereko ta ce ta yanke shawarar kin yin aure, domin ta fi son kula da ’ya’yanta da kuma lafiyarta.

Kara karanta wannan
Bauchi: Miji ya yi wa matarsa dukan tsiya har ta zarce lahira kan abincin Ramadan
“Idan na sake aure, da ba za ku yaba min ba, Kuma damuwar aure da jima’i na sa mace ta tsufa fiye da shekarunta.”
“Ban ma san yadda jin dadin namiji yake ba, Babu bukatar sake aure a rayuwata.”
Ta kuma yi bayani kan wahalhalun masana’antar fim, inda ta ce ta yi fina-finai goma ba tare da samun riba ba har sai da ta hadu da AbdulRazaq.
"Na sha wahala a masana'antar nan, Masu siyar da fim sun hana ni riba, amma AbdulRazaq ne ya ceci rayuwata, ya ba ni shawarwari masu amfani."
Game da cin hanci don samun rawa a fina-finai, ta ce babu wanda ya taba nemanta don haka inda ta shawarci matasan 'yan fim da su fara shirya nasu fina-finai ba tare da bata lokaci ba.
Hadiza Gabon ta caccaki masu sukarta
Kun ji cewa jarumar Hadiza Aliyu Gabon ta bayyana cewa duk wanda ya zage ta ko ya ɗauki alhakinta ba ta yafe ba duk da an shigo watan azumi.
Kalaman fitacciyar jarumar sun ja hankalin mabiyanta, wasu na ganin hakan bai dace ba kwata-kwata.
Asali: Legit.ng