Rahama Sadau Ta Gana da Ministocin Tinubu kan Shirin Bunkasa Al'adun Arewa

Rahama Sadau Ta Gana da Ministocin Tinubu kan Shirin Bunkasa Al'adun Arewa

  • Rahama Sadau ta gana da Ministan Tsaro na Ƙasa, Dr Bello Matawalle, a kan hadin gwiwa kan wani shiri na musamman da ta shirya
  • Fitacciyar jarumar ta kuma gana da Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris Malagi, domin tattauna a kan shirin
  • Shirin Arewa Turn Up da jarumar ke shiryawa ya kasance muhimmin taro da ta ke jagoranta domin baje kolin al’adun Arewa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta gana da ministocin tarayya domin neman goyon baya kan shirye-shiryen bunkasa harkar fina-finai da al’adu a Arewa.

Jarumar ta bayyana cewa tattaunawar ta kasance mai fa’ida, inda aka tattauna hanyoyin hadin gwiwa domin cigaban shirin.

Rahama Sadau ta gana da ministoci
Rahama Sadau ta gana da ministoci a Abuja. Hoto: Rahama Sadau
Asali: Facebook

Jarumar ta bayyana haka ne a shafinta na Facebook, inda ta gode wa ministocin bisa goyon bayan da suka nuna wa shirye-shiryenta.

Kara karanta wannan

Saukar farashi: Gwamna ya kawo shirin raba abinci kyauta a Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tattaunawar Sadau da ministan tsaro

Rahama Sadau ta gana da Ministan Tsaron Ƙasa, Dr Bello Muhammad Matawalle, domin tattauna hanyoyin haɗin gwiwa kan shirin baje kolin al'adun Arewa.

Jarumar ta bayyana cewa sun tattauna kan yadda za a amfana daga shirin cigaban matasa da bunkasa kirkire-kirkire.

Rahama Sadau ta kara da cewa Ministan ya yaba da shirye-shiryen Arewa Creative Workshop da Arewa Turn Up da take jagoranta.

Ana ganin hadin gwiwar zai taimaka wajen bunƙasa harkar fina-finai, al’adu da kuma baiwa matasa damar nuna ƙwarewarsu.

Sadau ta gana da ministan yaɗa labarai

Bayan haka, Rahama Sadau ta gana da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Alhaji Mohammed Idris Malagi.

A cewar jarumar, sun tattauna kan shirin Arewa Creative Workshop da kuma hanyoyin haɗin gwiwa domin inganta shi.

Ta bayyana cewa Ministan ya nuna goyon baya sosai ga shirin Arewa Turn Up, wanda ke ƙarfafa nishaɗi da al'adun Arewa.

Kara karanta wannan

"Tinubu mutumin kirki ne, yana da niyya mai kyau," Babban malami ya yi wa mutane Nasiha

Rahama ta ce irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen gabatar da al'adun Arewa ga duniya baki ɗaya.

Tarihin shirin da Rahama Sadau ta fara

Bincike ya nuna cewa Arewa Turn Up wani shiri ne da Rahama Sadau ta ƙirƙiro domin baje kolin al’adun Arewa.

An fara gudanar da taron a shekarar 2022, kuma ya samu gagarumar nasara, inda dubban matasa suka halarta.

Sakamakon nasarar da aka samu a shekarar farko, an shirya cigaba da gudanar da taron Arewa Turn Up a nan gaba.

Shirin Arewa Turn Up ya zama wani muhimmin taro a masana’antar fina-finai da nishaɗin Arewa, inda ake tallafa wa matasa da masu fasaha.

NNPCL
Rahama Sadau da wasu 'yan Kannywood yayin ganawa da jami'an kamfanin man Najeriya a makon da ya wuce. Hoto: NNPCL
Asali: Facebook

Rahama Sadau ta ce burinta shi ne ganin Arewa Turn Up ya zama wata babbar kafa ta bunƙasa al’adun yankin a duniya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

"Wa ya mata cikin?": Jarumar fim a Najeriya ta yi magana kan zargin sanata ya mata ciki

NNPCL zai yi hadaka da 'yan Kannywood

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya gana da wasu jaruman Kannywood a makon da ya wuce.

Legit ta rahoto cewa ganawar ta mayar da hankali kan yadda jaruman za su hada kai da NNPCL wajen wayar da kan al'umma kan makamashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng