Abubuwan da 'Yan Najeriya Suka Fada bayan Buhari Ya Yi Kyautar Daloli
- Wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ba wani mawaki kyautar dala, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce
- Ana hasashen cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi kyautar ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da gwamnan jihar Katsina ya jagoranta
- Masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana ra’ayoyi daban-daban kan wannan lamari, inda wasu suka yaba da wannan hali, yayin da wasu suka yi suka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya yi kyautar kudi a wani bidiyo.
Wannan abu ya ba mutane mamaki kasancewar Buhari ya shahara a matsayin shugaban da ba kasafai ake ganinsa a tarurrukan nishadi ba.

Asali: Getty Images
A bidiyon da Abdul Maje ya wallafa a TikTok, an nuna Buhari yana ba wani mawaki daga Arewacin Najeriya kyautar dala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, an gano Buhari yana mika dala ga mawakin tare da tafi bayan mawakin ya rera waka a harshen Hausa.
Ana hasashen lamarin ya faru ne a lokacin taron 'yan APC da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar Katsina, a dakin liyafa na shugaban kasa, ranar Asabar, 25 ga watan Janairu.
Buhari ya halarci taron APC a Katsina
Bayan barin ofis, Buhari ya koma Daura domin kula da gonarsa, sabanin wasu manyan 'yan siyasa da ke zaune a Abuja ko Lagos.
Taron APC da aka yi a jihar ya samu halartar wasu manyan baki da suka hada da Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina.
Haka zalika tsofaffin gwamnonin Katsina, Aminu Bello Masari da Ibrahim Shehu Shema, tare da tsofaffin mataimakan gwamnoni Alhaji Sirajo Umar Damari da Abdullahi Garba Faskari.
Malam Abdul Maje da ya wallafa bidiyon a TikTok bai bayar da karin bayani kan bidiyon ba ko adadin kudin da Buhari ya bayar.
Ra’ayoyin jama'a a kafafen sada zumunta
Lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta. Wani mai amfani da TikTok mai suna Suleiman Sudais Abdulsalam ya ce:
“Karon farko a tarihin duniya.”
Legit ta wallafa cewa wani mai suna Agbalaka 🏹, @CroBender, ya ce:
“Yadda suke kashe kudin al’umma kenan. Na zata tumaki da shanu ne kawai yake da su, ba dala ba.”
Habibu Bello Mayana, @The_HBMayana, ya ce:
“Karon farko, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba mawaki kyauta.”
Shi kuma Abdulrasheed, @ab_rashiid, ya ce:
“Wannan abu na da kyau, amma bai kamata ya kashe dala a gida ba. Wata kila kudin da ya dawo da su daga Paris ne. Ba shi da Naira kafin ya halarci taron.”
Wani kuma mai suna @dimkpa_prince ya rubuta:
“Ba su amfani da Naira kenan.”
Wani mai suna Šûčŕê pãpîťÓ LFC, @Menybah2, ya ce:
“Tsohon shugaban kasa yana kashe dala. Ba za ka taba ganin Obama yana kashe fam a Amurka ba.”
Shi kuwa Olasunkanmi Olapath, @AhmadKehindeOl1, ya ce:
“Karo na farko kenan da muka taba ganin Baba Buhari yana haka 🤣🤣🤣🤣.”
Gwamnatin Katsina za ta raba abinci
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Katsina ta yi alkawarin sayen abinci na Naira biliyan 9 domin rabawa talakawa.
Rahoton Legit ya nuna cewa mataimakin gwamnan jihar Katsina ya bayyana cewa za a raba abincin ne a watan Ramadan domin rage radadin rayuwa.
Asali: Legit.ng