Saurayi Ya Siyawa Wata Fitacciyar 'Yar TikTok Gidan N55m a Kano, Ta Saki Bidiyo
- Wani saurayi ya siya wa Maryam Sa'idu, fitacciyar 'yar TikTok gida na Naira miliyan 55, ya ce ba ya son ta ci gaba da zama a otel
- Maryam Sa'idu ta bayyana cewa gidan ya kunshi kayan Naira miliyan 22, tana mai bayyana dalilinta kin yin aure a wannan lokaci
- Bidiyon Maryam ya jawo ce-ce-ku-ce, inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu kan irin matakan da ta dauka na neman kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Saurayi ya gaji da zaman fitacciyar 'yar TikTok din Arewa, Maryam Sa'idu a otel, ya siya mata dankareren gida har na Naira miliyan 55.
Maryam Sa'idu ta shelanta cewa yanzu kwana a otel ya kare, za ta koma kwana a sabon gidanta mai dauke da kayan Naira miliyan 22.
Saurayi ya siyawa Maryam gidan N55m
A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, wanda Legit Hausa ta gani a shafin NIQABQUEEN na X, Maryam ta fadi yadda abin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fitacciyar 'yar Tiktok din, wadda aka gani tana magana a waya ta shaidawa wacce suke yin wayar da ita cewa:
"Waya ce maki aure ne na yi? Wallahi ba aure na yi ba. Saurayi na ya siya mani gida, ya ce ba ya son zamana a otel a Kano, ya siya mani gida ga shi nan.
"Ya siya mani gida na miliyan 55, ya sanya mun kaya na miliyan 22 a ciki."
'Yar TikTok ta ajiye batun aure a gefe
Wadda take wayar da ita, ta dage kan cewa 'yar TikTok din karya take yi mata, aure ta yi ne take boye wa, ita kuma Maryam ta dage kan cewa:
"Auren me, rufa mun asiri in yi aure yanzu, ai an daina yayi na."
Maryam Sa'idu ta shaidawa wadda suke wayar tare cewa "wallahi ba zan yi aure yanzu ba," saboda tana so a ci gaba da yayinta daga nan "har sai Tinubu ya sauka."
Mutane sun caccaki Maryam 'yar TikTok
Sai dai wannan bidiyo na Maryam 'yar TikTok da ya yadu a intanet ya jawo ce-ce-ku-ce mai zafi, inda wasu ke ganin cewa matashiyar ta yi nisan da ba za ta ji kira ba.
Wadda ta dora bidiyon, ta wallafa cewa:
"Irin yadda 'yan matan yanzu ke cire tsoro suna nuna cewa su karuwaine abin tsoro ne, suna fadin hakan da karfin zuciya. Allah ka shirya mana zuciya, ka sa mu fi karfin zuciyarmu."
Wasu daga cikin ra'ayoyin mutane da Legit Hausa ta tattaro suna cewa:
@Abbanafrah:
"Wato ni dai na rasa dalilin da yake saka namiji ajiye karuwa wai har ya saya mata gida da mota saboda zina, to ka aure ta mana kawai?
Ko dan mafi yawan masu yin haka kudin haramun su ke samu dole sai Allah ya jarabe su da bin hanyar shiga wuta."
@cute_eies:
"Abin da ke faruwa yanzu shi ne an ce ma abin nasu yaci gaba, da yawansu ta baya ake amfani da su shi ya sa ake ba su kudi masu yawa."
"Allah dai ya tsaremu da zuriyar mu ya tsare mana imaninmu."
@Being_umarh:
Rayuwa kenan. Wato tunanin mutuwa kadai mu ke yi har muke iya daina yin wasu abun, rashin sanin lokacin da za mu mutu ya isa ya zama dalilin mika lamuranmu ga Allah."
@FarouqEconomist:
"So yanzu an fara kyamar aure ana fiffita bariki. Karshen duniya."
Kalli bidiyon a kasa:
'Yar TikTok a Kano ta yi bidiyo tsirara
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata 'yar TikTok da ta shahara a Kano ta yi bidiyo tsirara haihuwar uwarta kuma an samu wani ya yada shi a soshiyal midiya.
Hukumar Hisbah ta bakin shugabanta, Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa ta ce ta samu nasarar cafke wannan 'yar TikTok tare da bayyana matakin da suka dauka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng