Wasu Fitattun Fina Finan Najeriya 5 da Ya Kamata Ku Kalla a Watan Disambar 2024

Wasu Fitattun Fina Finan Najeriya 5 da Ya Kamata Ku Kalla a Watan Disambar 2024

Disamba wata ne na farin ciki, soyayya, da haɗin kai. Hanya mafi kyau don jin daɗin wannan watan ita ce kallon fina-finan Kirsimeti na Nollywood masu cike da nishadi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Masu kallon fina-finai ta yanar gizo za su iya more waɗannan fina-finan da aka samar da su saboda murnar Kirsimeti a gida Najeriya.

Fina finan Nollywood 5 da ya kamata ku kalla a watan Disamba
'A Naija Christmas' da wasu fina finan Kudancin Najeriya da ya kamata ku kalla a Disamba. Hoto: Netflix
Asali: Facebook

Masu shirya fina-finai na Najeriya sun yi amfani da kwarewa wajen samar da fina finai biyar kan Kirsimeti da ke cike da dariya da ban tausayi, a cewar rahoton Tribune.

Wannan rahoton ya lissafo wasu daga cikin mafi kyawun fina-finan Kirsimeti na Nollywood da za su ba ku nishadi a wannan wata na Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. "A Naija Christmas" (2021)

Wannan fim ɗin, wanda Kunle Afolayan ya ba da umarni, ya zama abin sha'awar masu kallo.

Kara karanta wannan

"Za ku iya rasa rawaninku," Sarki Sanusi II ya fadi abin da ke barazana ga sarakai a Kano

An shirya labarin ne a kan wata uwa wacce burinta na Kirsimeti shi ne ganin 'ya'yanta sun yi aure.

Matsaloli masu ban dariya sun bayyana yayin da 'ya'yan suke ƙoƙarin cika burinta, inda suke kokarin daidaita soyayya, rayuwar iyali, da kuma bukukuwan Kirsimeti.

Ana iya kallon wannan fim din a shafin Netflix.

2. "Christmas in Miami" (2021)

Fitattun jarumai irin su Ayo Makun (AY) da Richard Mofe-Damijo (RMD) sun taka rawa a wannan fim ɗin, inda ‘yan Najeriya suka yi bikin Kirsimeti a Miami.

Fim ɗin yana ɗauke da al’adun ban dariya, rikicin iyali da kuma murnar bukukuwan Kirsimeti.

Christmas in Miami kashi na hudu ne na shirin fina-finan Nollywood na AKPOS wanda fitaccen jarumin barkwancin Najeriya AYO MAKUN wanda aka fi sani da 'AY' ya kirkira.

Ana iya kallon wannan fim a shafin Amazon ko a gidajen sinimu na Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matar El Rufai ta shiga tashin hankali, ta gamu da katuwar macijiya a gidanta

3. "Best Christmas Ever" (2022)

Best Christmas Ever fim ɗin Nollywood ne da aka yi shi a 2022, inda ya haska jarumai: Maurice Sam, Chinenye Nnebe, Sonia Uche, da Ebube Obio.

An shirya fim ɗin ne a kan Charlotte Sanders, wadda koyaushe take cikin ɗacin rai a lokacin Kirsimeti saboda tsohuwar kawarta Jackie tana aika mata wasiƙar labaran nasarorin da iyalanta suka samu kowacce shekara.

Wasu sun ce fim ɗin bai dace da yara ba saboda maganganun 'batsa' da kuma yanayin da ake iya jiyo gadon ma'aurata yana girgiza daga wani daki.

Ana iya kallon wannan fim a shafin YouTube.

4. "Silent Night" (2016)

Wannan fim ɗin ya ba da labari na soyayya da gyara kuskure yayin Kirsimeti.

“Silent Night” ya nuna ƙarfin yafiya da haɗin kai, yana nuna tasirin tausayi da kuma abubuwan nishadi da ban dariya a game da bukukuwan Kirsimeti.

5. "Merry Men: Another Mission" (2019)

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi martani yayin da jami'an tsaro suka mamaye fadar sarkin Kano

Fim ɗin na ɗauke da fitattun jarumai irin su Ramsey Nouah da Falz wadanda suka taka rawar da ta sanya fim din ya kayatu da kuma zama abin sha’awa a lokacin Kirsimeti.

A wannan Kirsimeti, ku sayi gugguru, ku dauki masoyanku, ku shiga gidajen kallon fina finai mafi kusa da ku, domin kallon fim din Merry Men: Another Mission.

Shafin Pulse.ng ya rahoto cewa fim din Merry Men: Another Mission ya samar da jimillar Naira miliyan 41.6 a makon farko da aka fara haska shi a gidajen sinimu.

Fitacciyar jarumar Nollywood ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa shahararriyar jarumar fina finan Kudancin Najeriya, Stella Ikwuegbu ta rigamu gidan gaskiya a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni.

Stella Ikwuegbu ta rasu ne tsakamakon ciwon daji da ya cinye kafarta kuma mutuwarta ta jefa mutane cikin jimami kamar yadda jarumi Stanley Nwoko ya sanar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.