Kwana Ya Kare: An Shiga Jimami bayan Sanar da Rasuwar Fitaccen Jarumin Fina Finai

Kwana Ya Kare: An Shiga Jimami bayan Sanar da Rasuwar Fitaccen Jarumin Fina Finai

  • Masana'antar shirya fina-finan Nollywood ta shiga jimami na rashin fitaccen jaruminta a yau Laraba a jihar Oyo
  • Marigayin mai suna Otunba Ayobami Olabiyi ya rasa ransa ne a birnin Ibadan da ke jihar bayan fama da rashin lafiya
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya sha fama da jinya na tsawon lokaci da ya dakile shi shirya fina-finai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - An shiga wani irin yanayi bayan sanar da mutuwar wani jarumin fina-finai a masana'antar Nollywood.

An tabbatar da mutuwar Otunba Ayobami Olabiyi a yau Laraba 16 ga watan Oktoban 2024 a birnin Ibadan a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

T-Pain da sauran sunaye 4 da aka lakawa Tinubu da dalilan alakanta shi da su

Fitaccen jarumin fina finai ya riga mu gidan gaskiya
Masana'antar fina-finan Nollywood ta yi rashin jaruminta a yau Laraba. Hoto: Otunba Ayobami Olabiyi.
Asali: Facebook

Jarimin fina-finai ya yi bankwana da duniya

The Nation ta ruwaito cewa marigayin da aka fi sani da Bobo B ya yi shura a masana'antar fina-finan Nollywood.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin rasuwarsa, Olabiyi shi ne tsohon shugaban kungiyar TAMPAN da jaruman fina-finai.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a yanzu marigayin shi ne sakataren kungiyar kafin ya yi bankwana da duniya.

Marigayin ya kasance cikin mummunan yanayi na rashin lafiya a yan kwanakin nan, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Yadda rashin lafiyar marigayin ta tsananta kwanaki nan

An tabbatar da cewa marigayin ya so shirya wani a watan jiya a jihar Oyo kafin rashin lafiyarsa ta munana.

An kwantar da marigayin ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Ibadan (UCH) a jihar Oyo inda ya ce ga garinku.

Shugabar kungiyar, TAMPAN, Bose Akinola ta tabbatar da mutuwar marigayin inda ta yi addu'ar Ubangiji ya yi masa rahama ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa.

Kara karanta wannan

Matar tsohon gwamna a Najeriya ta yi bankwana da duniya

Jarumin fina-finai, Shina ya kwanta dama

Kun ji cewa Masana'antar shirya fina-finan Nollywood a Najeriya ta shiga jimami bayan rasuwar Shina Sanyaolu a jihar Lagos.

Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba 11 ga watan Satumbar 2024 duk da ba a bayyana silar mutuwar fitaccen furodusan ba.

Jaruman fina-finan Nollywood da dama sun tura sakon ta'aziyya inda suka tabbatar da cewa Shina mutumin kirki ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.