Maulidi: Tarihi, Asali da Sauran Bayanai kan Sallar Gani da Za a Yi Kwanaki 3Ana Biki

Maulidi: Tarihi, Asali da Sauran Bayanai kan Sallar Gani da Za a Yi Kwanaki 3Ana Biki

  • Masarautar Gumel a jihar Jigawa ta fitar da sanarwa kan bikin Sallar Gani da ta saba yi duk shekara a lokacin Maulidi
  • Kamar yadda aka saba, masarautar ta ware kwanaki uku domin yin bikin a bana tare da kira a kan a zauna cikin shiri
  • Legit ta tattauna da wani mazaunin Jigawa domin jin yadda suke shirye shirye kan yadda za su halarci taron bikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Masarautar Gumel ta fitar da sanarwa kan yadda bikin Sallar Gani zai gudana a wannar shekarar.

Ana yin Sallar Gani ne a lokutan Maulidi sai dai akwai bambanci a kan yadda bikin ke gudana a Gumel da sauran wurare.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tallafin da za ta kaiwa mutanen Maiduguri

Sallar Gani
Za a yi Sallar Gani a Gumel. Hoto: Mai Katanga
Asali: Facebook

Majidadin Gumel, Alhaji Mustapha Aliyu ne ya tabbatar wa Legit yadda bikin Sallar Gani zai kasance a wannar shekarar.

Yaushe za a yi Sallar Gani a Gumel?

Masarautar Gumel ta bayyana cewa za a yi bikin Sallar Gani ne a tsawon kwanaki uku a shekarar 2024..

Kwanakin sun hada da ranar Jumu'a, Asabar da Lahadi wanda suka dace da 21, 22 da 23 ga watan Satumban 2024 da ake ciki.

Dalilin zaben kwanaki 3 domin Sallar Gani

Majidadin Gumel, Alhaji Mustapha Aliyu ya tabbatar da cewa a shekarun baya ana yin bikin ne a ranar Maulidi amma daga baya aka canza.

Alhaji Mustapha Aliyu ya ce an zabi cigaba da yin bikin ne a ranakun Juma'a, Asabar Lahadi na makon da aka yi bikin Maulid domin ba ma'aikata damar halartar bikin.

Kara karanta wannan

Kano: Aminu Ado ya sake daukar kansa Sarki, ya gayyaci Musulmi taron Maulidi a fadarsa

Sallar Gani a Gumel, Hadeja da Daura

A wasu wurare kamar Daura da Hadeja, ana yin Sallar Gani ne a ranar Maulidi har yanzu sabanin masarautar Gumel.

Haka zalika, Alhaji Mustapha Aliyu ya ce bikin Sallar Gani a Gumel ya samo asali ne daga al'adar Barebari wanda dama asalin masarautar Gumel ta Kanuri ce.

A wani bidiyo da Premier Radio ya wallafa a Facebook, Alhaji Mustapha Aliyu ya ce ana yin bikin ne a Gumel domin nuna shirin yaki da masarautar ke da shi.

Yadda ake Sallar Gani a Gumel

Sarki na fitowa a kan doki yayin bikin Sallar Gani ya zagaya gari kamar yadda ake a lokacin hawan Sallar Idi.

Haka zalika dukkan masu sarauta sukan caɓa ado domin su marawa sarki baya yayin bikin na tsawon kwanaki uku.

Legit ta tattauna da Aminu Taura

Wani mazaunin Jigawa, Amuni Taura ya zantawa Legit cewa a yanzu haka mutane sun fara shirye shiryen halartar taron a garin Gumel.

Kara karanta wannan

Yunwa: Wasu Gwamnonin jihohin Kudu sun fitar da tsarin wadata jama'a da abinci

Aminu ya ce mutane daga kananan hukumomi na neman abokan tafiya Gumel domin halartar Sallar Gani wanda suka saba yin hakan duk shekara.

Ya ce mutane daga kasashe da garuruwa daban daban dama suna dowowa zuwa gida domin halartar bikin.

An nada sabon sarkin Ningi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi ta ayyana Alhaji Haruna Yunusa Danyaya a matsayin sabon sarkin Ningi domin ya gaji mahaifinsa, marigayi Alhaji Yunusa.

Wata sanarwa daga mai ba gwamnan Bauchi shawara kan watsa labarai, Mukhtar Gidado, ta bayyana cewa Alhaji Haruna zai zama sarki na 17.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng