Ana Jimamin Mutuwar Basarake, Fitaccen Furodusa kuma Darakta Ya Rasu

Ana Jimamin Mutuwar Basarake, Fitaccen Furodusa kuma Darakta Ya Rasu

  • Masana'antar shirya fina-finan Nollywood a Najeriya ta shiga jimami bayan rasuwar Shina Sanyaolu a jihar Lagos
  • Marigayin ya rasu ne a jiya Laraba 11 ga watan Satumbar 2024 duk da ba a bayyana silar mutuwar ba
  • Jaruman fina-finan Nollywood da dama sun tura sakon ta'aziyya inda suka tabbatar da cewa Shina mutumin kirki ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Fitaccen furodusa kuma daraktan fina-finan Nollywood, Shina Sanyaolu ya kwanta dama.

Daraktan wanda ya kware wurin yin fina-finan Yarbanci ya rasu ne a jiya Laraba 11 ga watan Satumbar 2024.

Furodusa kuma daraktan fina finan Nollywood ya rasu
Daraktan fina-finan Nollywood, Shina Sanyaolu ya rasu. Hoto: @shinasanyaolu.
Asali: Instagram

Daraktan fina-finan Nollywood ya rasu

Shugaban kungiyar masu hada hotuna (TAMPAN), Bolaji Amusan shi ya bayyana haka a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

Bayan ambaliya a Borno da Bauchi, an shiga fargaba a garuruwan Yobe

"Ubangiji ya jikanka ya sa ka samu rahama kawu Sanyaolu Shina."

- Bolaji Amusan

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a bayyana ainihin silar mutuwar daraktan ba wanda ya ba da gudunmawa sosai a masana'antar.

Jaruman Nollywood da dama sun yi ta'aziyya

Jaruman masana'antar da dama sun bayyana kaduwarsu tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin.

Fitaccen jarumi, Jide Kosoko ya ce marigayin mutumin kirki ne wanda ya taba rayuwar mutane da dama.

Kosoko ya ce tabbas sun yi rashin mutum haziki wanda ya ba da gudunmawa mai tsoka ga harkar fina-finai.

Dattijon mai shekaru 70 ya ce rashin Shina a masana'antar shirya fina-finan Nollywood ba karamar gibi zai bari ba duba da yadda ya tallafawa mutane da dama.

Jarumin Nollywood ya koma gyaran famfo

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamna Zulum ya yi bayanin halin da ake ciki, ya faɗi kuɗin da Tinubu ya turo

Kun ji cewa fitaccen jarumi kuma mai shirya fina-finan Nollywood a Najeriya, Chris Bassey, ya bayyana cewa ya sauya sana'a bayan ya koma kasar Canada.

Jarumi Bassey ya ce ya hakura da daukakar da ya ke da ita a harkar fim, ya kama sana'ar gyaran famfo tun bayan komawarsa Canada.

A zantawarmu da Abdul M. Shareef, wani jarumi a masana'antar Kannywood, ya koka cewa matsin tattali ya shafi harkar fim a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.