Sun Jawo An Goge Shafinsa a Facebook, Rarara Ya Caccaki 'Yan Bakin Ciki' a Sabuwar Waka
- Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya fitar da sabuwar wakar martani bayan goge shafinsa na Facebook da aka yi
- Bisa alamu wakar martani ce ga wadanda suka yi taron dangi a kan mawakin inda yake nuna hassada aka masa a kan yabon Bola Tinubu
- An goge shafin Dauda Kahutu Rarara ne bayan ya yi sabuwar wakar yabon shugaba Bola Tinubu ana tsaka da tsadar rayuwa da kunci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya yi sabuwar waka bayan toshe masa shafin Facebook a kan Bola Tinubu.
Ana ganin cewa Dauda Kahutu Rarara ya yi wakar ne bisa martani bayan toshe masa shafin Facebook.
Legit ta tattaro maganganun da Dauda Kahutu Rarara ya yi a cikin wakar ne a wani bidiyo da Dan Kaka ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabuwar wakar Rarara mai suna 'Mutumin banza'
Amshin sabuwar wakar da Dauda Kahutu Rarara ya yi shi ne mutumin banza inda shi da masu amshi ke rerawa.
Yan Najeriya da dama sun nuna takaici a kan amshin suna zargin cewa da su yake, musamman wanda suka ba da hadin kai wajen toshe masa shafin Facebook.
'Ana mani hassada' - Rarara a sabuwar waka
A cikin wakar, Dauda Kahutu Rarara ya ce ana masa yi hassada amma duk da haka yana nuna zurfin ciki.
Shahararren mawakin ya ce Allah ya masa baiwa kuma ba yadda aka iya da shi, ya zama ɗan hakkin da aka rena.
Habaicin 'da kai na ke' a wakar Rarara
Al'ummar Najeriya suna cigaba ruɗani kan da wa Rarara ya ke amma ya ambaci cewa duk wanda ya tsargu da shi ya ke.
A karshe, Dauda Kahutu Rarara ya kara da cewa shi kamar gamji ya ke, ana saransa yana kara toho wa.
Rarara: 'Ina bayan Bola Tinubu'
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahuta Rarara ya bayyana cewa ba zai taba daina nuna goyon bayansa ga shugaban kasa, Bola Tinubu ba.
Rarara ya fadi haka ne a martani kan yadda jama'a ke caccakarsa, musamman bayan ya saki sabuwar waka da ke goyon bayan shugaban kasa Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng