"Ku Kara Hakuri": Bidiyon Umar Bush Yana Ba da Tabbacin Samun Sauki Bayan Shiga Ofis
- Ɗan barkwanci mai ashariya, Umar Bush ya shiga ofishinsa a hukumance bayan nada shi hadimi na musamman a bangaren nishadi a Abuja
- Umar ya shiga ofishin ne a yau Talata 16 ga watan Yulin 2024 inda ya roki ƴan Najeriya su kara hakuri komai zai yi sauki
- Wannan na zuwa ne kwana guda bayan Bush ya zama mai ba da shawara na musamman a bangaren nishadi ga hadimin Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shahararren mai barkwanci a Arewacin Najeriya, Umar Bush ya shiga ofishinsa a Abuja bayan samun mukami.
Bush ya shiga ofishin ne a yau Talata 16 ga watan Yulin 2024 kwana daya bayan nada shi mai ba da shawara na musamman a bangaren nishadi ga hadimin Bola Tinubu.
Umar Bush ya ba 'yan Najeriya hakuri
An gano Umar Bush a wani faifan bidiyo da @mr_kams ya wallafa a shafin X yana magana tare da ba 'yan Najeriya hakuri kan halin da ake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umar Bush ya roki ƴan kasar su kara hakuri komai zai dawo daidai kamar yadda ake bukata.
Ya ce Allah ne kadai zai kawo dauki bayan wani a gefe ya yi masa shagube da cewa shi ne zai 'yan kasar saukin?.
"Al'ummar Najeriya sauki yana nan tafe, ku kara hakuri sauki zai zo gare ku."
- Umar Bush
Umar Bush ya caccaki abokin tafiyarsa
Umar Bush ya yi zazzafan martani bayan wani a gefe ya tambaye shi shi zai kawo saukin ne ga ƴan Najeriya, sai Umar ya ce:
"Sauki Allah ne zai kawo ba uba*ka ne zai kawo ba."
Bush cikin fushi ya gargade shi da ya yi hankali inda ya ce bai yadda da abin da ya masa ba.
Bidiyon Umar Bush yana ganawa da Dangote
A wani labarin, kun ji cewa dan Arewa da ya yi shuhura wajen dura ashariya ga abokin tafiyarsa, Umar Bush ya samu damar shiga fadar shugaban kasa a wata gayyata.
A cikin bidiyo an gano lokacin da Bush da ‘yan tawagarsa ke cikin Villa, inda ya gamu da wasu fitattun ‘yan Najeriya ciki har Aliko Dangote.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng