Shahararren Mai Barkwanci a Arewa, Umar Bush, Ya Samu Mukami a Gwamnatin Tinubu

Shahararren Mai Barkwanci a Arewa, Umar Bush, Ya Samu Mukami a Gwamnatin Tinubu

  • Fitaccen mai barkwanci a Arewa, Umar Bush ya tabbata mai bada shawara na musamman ga mai ba wa Shugaban kasa shawara kan masu bukata ta musamman
  • Umar Bush dai zai rika yada manufar ofishin da yake karkashinsa ta hanyar yin tallace-tallace da inganta alakarsa da jama'a a kafafen sada zumunta
  • Wannan nadin ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu ke ganin cewa yanzu a Najeriya gara ka haukace sai ka samu matsayi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fitaccen mai barkwancin nan daga Arewa, Umar Bush ya samu mukamin mai tallafawa Hon. Mohammed Abba Isah kan harkokin nishadi.

Hon. Mohammed Abba Isa shi ne babban mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan masu bukata ta musamman da kuma rashin nuna bambanci.

Kara karanta wannan

"Na yi mamakin ganin abin da ban yi tsammani ba": Rarara kan sace mahaifiyarsa

Mai ba Shugaba Tinubu shawara ya nada Umar Bush wani muhimmin mukami
Umar Bush, fitaccen mai barkwanci daga Arewa ya samu mukami a gwamnatin Tinubu. Hoto: @dammiedammie35
Asali: Twitter

Umar Bush ya samu mukamin siyasa

An tabbatar da wannan nadin a takardar nadin da aka gani mai dauke da lamba SSAP/SNEO/24/VOL.1/464 wadda aka aikawa Umar Dan Kawu, wanda aka fi sani da Umar Bush, inji rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takardar mai dauke da taken: "Sanarwar nadin mai tallafawa na musamman kan nishadi," ta nuna amincewar Hon. Mohammed Isa da nadin Umar Bush matsayin mai tallafa masa.

Ayyukan Umar Bush sun hada da kula da yada manufofi a shafukan sada zumunta, inganta alakar ofishinsa da jama'a, da kuma yin talluka da za su tallata manufofin ofishinsa.

Nadin Umar Bush ya fara aiki ne daga ranar 10 ga Yuli, 2024, na tsawon wa'adin shekaru biyu, tare da yiwuwar sabunta nadin, amma ya danganta da irin kwazon da ya nuna.

Mutane sun yi martani kan nadin Bush

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure tsakanin fitacciyar jarumar Kannywood da mabiyanta a soshiyal midiya

Wannan nadin da aka yi wa Umar Bush ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta wanda mu ka tattaro kadan daga ciki.

@kwenAisha ta ce:

"Ina taya ka murna kan nadin da aka yi maka Alhaji Umar Bush a matsayin mai bada shawara ta musamman ga mataimaki na musamman kan nishadi ga Shugaban kasa kan masu bukata ta musamman."

@el_bonga ya ce:

"Umar Bush wanda babban tambarinsa shi ne kutuntuma zage-zage a yanar gizo an nada shi mai bada shawara na musamman kan nishadi.
"Yayin da Khalifa Aminu wanda ya kirkiro fasahar taimakawa makafi su yi tafiya babu sanda aka yi watsi da shi. Al'ummarmu na sakawa shirme fiye da fikira"

@Bashir_GS ya ra'ayinsa da cewa:

"Ina farin ciki da Umar Bush ya samu wannan mukamin, a kalla yanzu zamu fahimci irin mutanen da ke rike da mukamai. Kasar kanta ba ta masu saiti bace."

@Dr_dabo1 ya damu da nadin Umar Bush:

Kara karanta wannan

Shin da gaske an aikawa malamai N16m domin hana matasa zanga-zanga a Arewa?

"Wannan mutumin Umar Bush ne aka nada mai bada shawara na musamman kan Nishadi ga shugaban kasa, ina tunanin mutane masu hankali ne kadai ke wahala a kasar nan."

@Ashman__jr ya bayyana ra'ayinsa da cewa:

"Hanya daya da zaka zama sananne a Najeriya shi ne ka haukace. Allah ya kara lafiya Umar Bush."

A cewar @Saeed__manager:

"An ba wa Umar Bush mai bada shawara na musamman kan nishadi ga mai bada shawara ga shugaban kasa kan lamurran masu bukata ta musamman.
"Toh jama'a zan fada da babbar murya, hauka ya yi rana, yanzu ta fi shegiyar digiri."

An soki gwamnati kan nadin Umar Bush

A zantawarmu da wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum a Facebook, Usman Muhammad Audi, ya ce abin da gwamnati ta yi bai dace ba.

Usman Audi ya ce:

"An ba Umar Bush wanda ya kware a zagin mutane mukami yayin da injiniya Khalifa Aminu, wanda ya kirkiri wata na'ura mai taimakawa makafi, bai sami irin wannan girmamawa ba.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun soki Ministan Buhari kan goyon bayan zanga zanga

"Abin damuwa ne cewa mutane kamar Khalifa Aminu, wadanda suke bayar da muhimman gudunmawa, ana watsi da su yayin da irinsu Umar Bush suke karɓar yabo da ya fi kima."

Tinubu ya warware nadin shugaban HYPREP

A wani labari na daban, mun ruwaito muku yadda ta leko kuma ta komawa Olufemi Adekanmbi a matsayin sabon shugaban HYPREP.

Tinubu dai ya nada shi shugaban HYPREP ne amma baya kwanaki biyu ya kwace tare da dawo da tsohon shugaban, Farfesa Zabbey.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.