Wakar Atiku ta 2027: Mawaki Rarara ya Watsar da APC? Gaskiya ta Bayyana

Wakar Atiku ta 2027: Mawaki Rarara ya Watsar da APC? Gaskiya ta Bayyana

  • Masu amfani da kafafen sada zumunta sun fara tofa albarkacin bakinsu kan wani bidiyon Rarara
  • A bidiyon, ana iya ganin Dauda Kahuta Rarara amma wakar Atiku Abubakar ta na tashi, inda wasu ke ganin ya sauya sheka
  • Hadimin Rarara kan kafafen sada zumunta, Rabi'u Garba Gaya ya ce ba muryar mai gidansa ba ce, dan kwaikwayo ne

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun fara yada bidiyo mawaki Dauda Kahuta Rarara da cewa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP. Mawaki Rarara dai shararren dan APC ne da ya dade ya na wake jiga-jigan jam'iyyar ciki har da Abdullahi Ganduje da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: 'Yan sanda sun yi ram da iyayen da suka saka ɗansu a kasuwa

Rarara
An gano wanda ya yi wakar Atiku da muryar Rarara Hoto: Dauda Kahuta Rarara/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A wani bidiyo da wani mai amfani da shafin X, @Tkr__khalifa ya wallafa, an jiwo murya mai kama da ta Rarara na wake Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP

Rarara ne a bidiyon wakar Atiku?

A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an hango mawaki Rarara da 'yan amshinsa ciki har da Aisha Humairah su na waka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A na jiyo tashin wakar 'mu dai Atiku zabinmu' daga bidiyon da wata murya da aka hakikance ta Rarara ce.

Tuni masu amfani da shafin X su ka fara martani, inda wasu ke ganin zafin sace mahaifiyar mawakin ce ta sa shi yin wakar.

@KakoNafiu ya ce;

Sbaida an sace babar sa. Sai yanzu yasan ana sace iyaye kenan. To allah ya bayyana ta

@Anas_Sulaiman_I ya ce;

wallahi na yarda Rarara kahutu yafi buhari wulakanchi

Kara karanta wannan

Kano: Sadakar N100,000 ya saka magidanci sake matarsa a gadon asibiti

@MuhammahBaye ya ce;

Atiku is coming very soon Insha Allah

@TalberOy ya ce;

Wannan ba murya rarara bace

"Ba muryarsa ba ce," Hadimin Rarara

Mataimaki na musamman ga Dauda Kahutu Rarara a kan kafafan sada zumunta, Rabi'u Garba Gaya ya musanta cewa mai gidansa ne a bidiyon wakar da ke yawo. Ya shaidawa Legit cewa tabbas bidiyon Rarara ne, amma wakar ba shi ya yi ta ba, wani mawaki da ke kwaikwayonsa.

Wannan bidiyon wakar Fatima mai Zogale ce, wakar kuma ba Rarara ne ya yi ba. S. Alkadir sunan wanda ya yi wakar, dama shi dan PDP ne.

- Rabi'u Garba Gaya

Farfesa ya fallasa masu daukar nauyin Tara

A wani labarin kun ji cewa Farfesa Abdullahi Uba Adamu na jami'ar Bayero da ke Kano ya fallasa wadanda ke daukar nauyin wakokin Rarara.

Farfesan ya kara da cewa ba zai zama abin mamaki ba nan gaba a jiyo shi ya na 'zagin' jigo a APC, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sanda sun gano yarinya mai shekaru 2 da aka sace a makota

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.