"Na yi Nadamar Fifita Soyayya a kan Kuɗi," Jarumar Nollywood Yvonne Jegede
- Fitacciyar jarumar Nollywood Yvonne Jegede ta bayyana manyan dalilai guda biyu da su ka raba ta da mijinta, jarumi Olakunle 'Abounce' Fawole shekara ɗaya kacal da aurensu
- Yvonne Jegede ta bayyana cewa tsohon mijinta baya kawo isassun kudi wajen tafiyar da gida, sannan idan ta yi masa wasa ko 'yar zolaya, ya na dauka da zafi
- Jarumi Olakunle Fawole ya angonce da Yvonne Jegede a shekarar 2018, kuma sun rabu a shekarar 2019 da yaro daga a tsakaninsu duk da bambancin shekaru takwas tsakaninsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nigeria- Fitacciyar jarumar Nollywood, Yvonne Jegede ta bayyana wasu daga dalilan rabuwar aurenta da jarumi Olakunle 'Abounce' Fawole. A wata hira da jarumar ta yi, ta ce matsalar kuɗi na daga jiga-jigan dalilan rabuwar aurensu domin nauyin ya rataya a wuyanta.
The Nation ta wallafa cewa jarumar ta ce ita ce ke kawo kaso mafi tsoka na kuɗin amfanin gida, lamarin da ya sa ta ke ganin da ta fifita kuɗi a ka n soyayya da haka ba ta faru ba.
"Fawole bai san wasa ba," Yvonne
The Herald ta wallafa wasu dalilan da jaruma Yvonne Jegede ta ce sun kashe mata aure, daya daga ciki shi ne tsohon mijinta bai san wasa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ta ɗora laifin hakan kan bambancin shekarun da ke tsakaninta da Fawole.
Jarumar fim din ta ce idan ta yi masa wasa, ya na fahimtarsu kamar raini, wanda sam ita kuma ba haka ta ke nufi ba. Wannan shi ne karon farko da jaruma Yvonne Jegede ta magantu kan rabuwarta da Fawole tun bayan rabuwarsu a shekarar 2019, shekara ɗaya tal bayan aurensu.
Jarumar Nollywood Tacha ta sanya rigar N140m
A baya kun samu labarin jarumar Nollywood Natacha Anita Akide ta kece raini yayin da ta sanya rigara N140m zuwa taron raba kyaututtuka ga 'yan fim a Afrika na AMVCA.
Wannan ba shi ne farau ba, domin a taron na AMVCA a shekarar 2023, tauraruwar BBNaija Tacha ta sanya rigar $20,000.
Asali: Legit.ng