Mata 'Yar Najeriya Ta Koka Bayan Lauyar da Ta Sa Mijinta Ya Saketa Ta Yi Wuff da Shi

Mata 'Yar Najeriya Ta Koka Bayan Lauyar da Ta Sa Mijinta Ya Saketa Ta Yi Wuff da Shi

  • Wata bazawara ta shiga damuwa bayan ta gano tsohon mijinta da ya sake ta ya auri lauyanta bayan gama shari'a a kotu
  • Lauyar ita ce ta wakilce matar a yayin da take neman saki a wajen tsohon mijinta a kotu, sannan bayan ƴan makonni ta yi wuff da shi
  • Ƴan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta kan lamarin inda da yawa daga cikinsu suka goyi bayan lauyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wata mata ƴar Najeriya ta koka bayan ta samu labarin cewa tsohon mijinta ya auri lauyar da ta wakilce ta a kotu

Ojong Agbor ne ya watsa labarin auren a shafinsa na Facebook.

Lauya ta auri mijin matar da ta sa ya saki
Matar aure ta koka bayan lauya ya auri tsohon mijinta (Hoton an yi amfani da shi ne kawai domin misali) Hoto: Gorodenkoff, Bloomberg
Asali: Getty Images

Mata ta koka bayan lauyanta ta auri tsohon mijinta

Kara karanta wannan

Komai nisan jifa: Matashi ya shiga hannun jami'an tsaro bayan shekaru da damfara

A cewar Ojong, lauyar ita ce ta wakilci matar a ƙarar da ta shigar da tsohon mijinta tana neman ya sake ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sati biyu bayan an yi sakin, sai lauyar ta yi wuff da tsohon mijin matar.

Ojong ya rubuta cewa matar ƴar jihar Akwa Ibom ce.

Ya rubuta:

"Lauyar da ta taimaka min wajen gudanar da shari’ar saki na ta auri tsohon mijina makonni biyu bayan kammala shari’a a kotu."
"Bazawara daga birnin Uyo na jihar Akwa Ibom ta koka."

Ƴan Najeriya sun mayar da martani kan lamarin

Genevieve Ojong Ijoko ta rubuta:

"A baya an taɓa faɗin cewa a je harabar kotu mutum zai iya samun miji ko mata. Mutane da dama na kokawar su fito daga gidan aure wasu na ƙoƙarin su shiga. Yanzu waye zai ceto mu?"

Kara karanta wannan

NLC: Muhimman abubuwan da aka tattake wuri a kansu a taron mafi ƙarancin albashi

Elizabeth Akakar ta rubuta:

"Dama mace abokiyar gabar ƴar uwarta mace ce. Mata ku yi hattara."

Angien Endurance ya rubuta:

"Ba ta gode da ni'imar da ubangiji ya yi mata ba, wata ta karɓi ni'imar."

Elizabeth Jimmy ta rubuta:

"Ina tunanin kin sake shi, to menene abin kuka kuma."

Moses Edim ya rubuta:

"Mutum ba ya sanin muhimmancin abin da ke hannunsa har sai ya suɓuce masa."

Donald Omang ya rubuta:

"Ki yarda da ƙaddararki ki manta da komai. Ubangiji zai baki daidai da ke."

Kotu ta raba aure

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kotun shari'ar Musulunci a jihar Kano ta raba auren da aka ɗaura tsakanin wani direba, Zakari Ghali, da Shamsiyya Haruna kan dalilin rashin zama wuri ɗaya.

Tun da farko Shamsiyya Haruna da ke zama a Unguwa Uku Quarters a jihar Kano ta shigar da ƙara gaban kotun Musulunci, inda ta roƙi alkali ya kashe aurenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng