Gwamnati ta Haramta Nuna Tsafin Kudi a Fina finan 'Nollywood'

Gwamnati ta Haramta Nuna Tsafin Kudi a Fina finan 'Nollywood'

  • Hukumar dake tsaftace fina-finan ta kasa, NFVCB ta haramta nuna duk wani abu da ya danganci tsafin kudi da rashin tarbiyya a cikin shirye-shiryen da Nollywood ke yi
  • Babban darakta a hukumar, Dr Sha'aibu Husseini ne ya bayyanawa masu ruwa da tsaki a harkar fina-finan cewa daga yanzu gwamnati ba za ta lamunci nuna tsafi ba
  • Ya kara da cewa daga abubuwan da aka haramta nunawa akwai shaye-shaye da busa tabar sigari domin tsaftace tarbiyyar matasan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Enugu-Hukumar da ke tace fina-finai ta kasa (NFVCB) ta haramta nuna duk wani yanayi da ke nuna tsafin kudi a fina-finan Nollywood.

Kara karanta wannan

"Yadda Tinubu ya bi ya hana tattalin arzikin Najeriya durkushewa", Kashim Shettima

Babban daraktan hukumar, Dr Shaibu Husseini, ne ya bayyana haramcin, tare da hana nuna duk wani abu da zai kara gurbata tarbiyyar matasan kasar nan.

Daukar fim
Gwamnati ta yi dokar hana nuna tsafi a fina-finai Hoto: MCT
Asali: Getty Images

Daily Trust ta tattaro cewa babban daraktan ya bayyana haka ne yayin taron masu ruwa da tsaki domin kakkabe busa sigari a fina-finai da ya gudana a ranar Laraba a jihar Enugu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hana nuna tsafi zai tsaftace fina-finai?

Babban daraktan hukumar NFVCB, Dr Shaibu Husseini ya bayyana cewa sun ga bukatar haramta nuna tsafin kudi, shaye-shaye da sauran ayyukan bata gari domin tsaftace fina-finan da tarbiyyar matasa.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa tsohon ministan yada labarai na kasa, Alhaji Lai Muhammad ne ya ga dacewar daukar matakin.

Ya ce Ministar Al’adu da Kirkira, Hannatu Musa Musawa ta amince da dokar da ta haramnata tsafin kudi, kisa don tsafin kudi, amfani da sigarin da makamantansu.

Kara karanta wannan

NAHCON ta faɗi dalilin rashin fara jigilar alhazan Kano da wasu jihohi 6, ta gama da Nasarawa

Dr Shaibu Husseini ya kara da cewa tuni suka aikewa da ma’aikatar shari’a da dokar domin adanawa.

Ali Nuhu ya zama shugaban NFC

Mun ruwaito muku labarin cewa fitaccen dan wasan kwaikwayo da ya fara tashe daga Kannywood, Ali Nuhu ya zama shugaban hukumar fina-finai ta kasa NFC.

Ali Nuhu ya zama shugaban hukumar ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadinsa, kuma tuni ya yi alkawarin kama aiki gadan-gadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel