iPhone 14 Pro Max vs Samsung S22: Wani Da Abokansa Sun Tsinduma Wayoyinsu A Ruwa Don Gwada Wacce Ta Fi Ƙarko

iPhone 14 Pro Max vs Samsung S22: Wani Da Abokansa Sun Tsinduma Wayoyinsu A Ruwa Don Gwada Wacce Ta Fi Ƙarko

  • Bidiyon tawagar wasu abokai da ke kokarin gwada tsawon lokacin da wayarsu za ta yi cikin ruwa ya sa wasu da dama na jinjinawa Samsung S22
  • Abokan sun tattaro wayoyinsu da suka hada da iphone 13, 14 pro max da Samsung S22+, suka saka dukkansu cikin ruwa a roba
  • Mutane da dama sun ga lokacin da aka tsamo wayoyin daga ruwan bayan yan mintuwa don latsa sikirin a gwada amfani da su

Wani matashi, @her.ex_boyfriend,_, da abokansa sun dauki hankulan mutane da dama yayin da suka saka wayoyinsu na iPhone 14 pro max, iPhone 13 pro max, da Samsung S22 a cikin mazabi da ruwa.

Mutumin da ya wallafa bidiyon ya ce suna son su gwada wacce cikin wayoyin ta fi karko a bangaren jure ruwa.

Kara karanta wannan

Amarya Da Ango Sun Keta Daji a Kafa Zuwa Wajen Daurin Aurensu, Bidiyonsu Ya Yadu

Iphone vs Samsung
An saka iPhone da Samsung cikin ruwa, mutane sun jinjinawa Samsung bayan gasar. Hoto: @her.ex_boyfriend
Asali: TikTok

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wacce ta fi karko tsakanin Samsung S22 da iPhone 14?

Bayan sun saka wayoyinsu masu tsada a cikin ruwa, sun yi amfani da agogo sun saka lokaci. Bayan minti daya, wayoyin iPhone din sun dauke wuta.

A wani bidiyo daban, dukkansu sun ciro wayoyinsu daga ruwa. Dukkan wayoyin na aiki. Da suka gwada latsa wayoyin, sun ce Samsung S22 ya fi aiki da kyau.

Kalli daya cikin bidiyonsu a kasa:

A lokacin hada wannan rahoton, a kalla mutane 500 sun yi tsokaci a kan bidiyon, sannan mutum kimanin 24,000 sun latsa like.

Legit.ng ta tattara wasu cikin tsokacin da mutane suka yi a kasa:

@user1192816006748 ya ce:

"Samsung ba na yara bane iPhone kawai iya kwaliya ne."

@ADOS cewa ya yi:

"Samsung bai san cewa lokaci ya fara ba."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Ginin da Abba Gida-Gida Ya Fara Rusawa Ya Danne Mutane a Kano, Wani Ya Mutu

@Smart ya ce:

"Samsung ne kan gaba wurin hana ruwa shiga waya."

@L.E.crown ya rubuta:

"Samsung zai iya kasancewa cikin ruwan har gobe."

@MiNiSter ya ce:

"Ba ku tsoro fa, tsoro ba zai bar ni in kai iPhone 14 pro di na kusa da ruwa ba."

@Peter Urgent ya yi tsokaci:

"Ga masu cewa Samsung, kawai sun saita hasken sikirin din ne kar ya mutu har sai kimanin minti 5."

@Isabella ya ce:

"Yara masu ganganci."

@Kenny wealth ya rubuta:

"Ina gyaran waya fa ko da ya fara bada matsala."

@Sunuusi Alfa ya ce:

"Samsung ita ce kan gaba amma ya kamata ka kwatanta s23 ne da 14pro max."

@user1192816006748:

"Na ce Samsung ba wayan yara bane amma iPhone duk kwaliya ne."

Kana iya amfani da WhatsApp ko wayarka ba ta kunne

A wani rahoton, kun ji cewa manhajar WhatsApp mallakar kamfanin Meta ta ce ta fara wani gwaji da zai ba wa masu amfani da manhajar ikon amfani da ita ko wayarsu na kashe.

Kara karanta wannan

Jarumi Kuma Mutum Mafi Tsawo a Najeriya, Afeez Agoro, Ya Rasu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164