'Za ka iya amfani da Manhajar WhatsApp ko da wayarka na kashe'

'Za ka iya amfani da Manhajar WhatsApp ko da wayarka na kashe'

  • Mutane za su samu damar fara amfani da manhajar WhatsApp ko da wayarsu na kashe
  • Kamfanin Facebook wacce ke da manhajar WhatsApp ne ta fitar da wannan sanarwar
  • Masu amfani da manhajar na WhatsApp za su samu tsaro idan sun bude manhajar a wasu na'urorin da ba wayansu ba

Manhajar aika saƙon kar ta kwana na WhatsApp mallakar kamfanin Facebook ta sanar da fara wani gwaji da zai bawa masu amfani da manhajar daman amfani da ita ko da wayarsu na kashe, The Punch ta ruwaito.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta a ranar Laraba, Injiniyoyi a Facebook sun ce sabon tsarin zai bawa mutane daman amfani da WhatsApp a wasu na'urorinsu ba tare da sun sada na'urar da wayarsu ta salula ba.

DUBA WANNAN: Hoton Yadda Aka Yi Jana'izar Janar Na Sojan Nigeria Da Ƴan Bindiga Suka Kashe

'Za ka iya amfani da Manhajar WhatsApp ko da wayarka na kashe'
'Za ka iya amfani da Manhajar WhatsApp ko da wayarka na kashe'. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Rubutun da aka wallafa ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta gyara dokar kisa, an sa hannu a fara rataye masu garkuwa da mutane

"Wannan sabon cigaban, za ka iya amfani da WhatsApp a wayarka da wasu na'urori hudu daban wadanda ba waya ba a lokaci guda - koda batirin wayarka ya mutu."

Tunda aka samar da shi a 2009, Facebook ta siya manhajar aika sakonnin a wayoyin zamani, WhatsApp, wanda ke da biliyoyin masu amfani da shi a faɗin duniya.

Tun a baya ana iya amfani da WhatsApp a wasu 'na'urorin' kamar kwamfuta, amma yana aiki ne kawai idan wayar mutum yana kunne kuma akwai sabis.

Wasu matsaloli na iya tasowa kamar katsewar sabis ɗin sau da yawa.

KU KARANTA: IPOB Ta Bayyana Gwamnoni 2 Da Minista Da Suka Ɗauki Nauyin Kamo Nnamdi Kanu

Sabon cigaban da aka samu a WhatsApp ya kawar da wannan ƙallubalen tunda baya bukatar sadarwa tsakaninsa da wayarka kafin ya yi aiki, a cewar kamfanin.

Facebook ya ƙara da cewa mutane da dama za su samu damar amfana da wannan sabon tsarin a yayin da ake ƙara inganta shi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dagacin kauye ya kai kuka game da harin da Dorina ke kaiwa kaiwa mutane a Gombe

Ya kuma kara bada tabbacin cewa dukkanin matakan tsaron kare bayannan da WhatsApp ke da shi za su yi amfani a sabbin na'urorin.

"Ko wanne na'ura zai yi aiki da WhatsApp ɗin ka yana mai cin gashin kansa yayin da za a samar da tsaro to yadda kai da wanda ka tura wa saƙon ne kawai zaku iya sanin abin da kuka aika kamar yadda masu amfani da WhatsApp suka sani."

Gwamnatin tarayya ta kebance kimanin bilyan 5 don bibiyan Whatsapp din yan Najeriya

A wani labarin daban, gwamnatin tarayya ta ajiye kimanin bilyan 4.8 ga hukumar leken asirin Najeriya (NIA) domin bibiyan abubuwan da yan Najeriya ke tattaunawa a WhatsApp da kuma salular Thuraya.

WhatsApp wata manhaja ce da mutane ke tattaunawa da 'yan uwa da abokan arziki.

WhatsApp mallakin kamfanin Facebook ne dake jihar California a Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164