"Za A Kama Ka Ranar Juma'a", Yan Sanda Suka Fada Wa Shahararren Mawakin Najeriya Portable
- Yan sandan Najeriya sun ce za su kama mawaki, Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable a ranar Juma'a
- Abimbola Oyeyemi, kakakin yan sanda Ogun ya ce an gayyaci Portable sau biyar ya kawo kansa amma ya ki zuwa shi yasa aka tura masa jami'ai ranar Talata
- Kakakin yan sandan ya ce wani mai sutudiyo ne ya yi korafin cewa Portable da yaransa sun lakada masa duka, sun rufe masa sutudiyo kuma ake bincike
Ogun - Rundunar yan sandan Najeriya ta jihar Ogun ta ba wa fitaccen mawakin gambara, Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, awa 72 ya kai kansa ofishinta mafi kusa ko kuma a kama shi a ranar Juma'a, rahoton Daily Trust.
Wasu bidiyo biyu sun yadu a dandalin sada zumunta da ke nuna mawakin yana dura wa wasu jami'an yan sandan Najeriya ashar.
A bidiyon, Portable ya yi ikirarin cewa masu zamba ta intanet ne suka turo yan sanda zuwa mashayarsa don kama ma'aikatansa 'ba tare da wani dalili ba.'
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Idan ba ka kawu kanka cikin awa 72 ba, za mu kama ka, Yan sanda ga Portable
Kakakin yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da cewa rundunar ta bawa mawakin awa 72 ya kai kansa hannun hukuma ko a kama shi.
Oyeyemi ya yi bayanin cewa yan sandan sun so kama shi ne bayan tura masa gayyata sau biyar da guda ta hannun mahaifinsa amma duk bai amsa ba.
Dalilin da yasa muka gayyaci Portable - Oyeyemi
Kakakin yan sandan ya kara da cewa an gayyaci Portable ne saboda wani matashi mai sutudiyo ya kai korafi yana ikirarin Portable da yaransa sun masa dukan tsiya sun kuma rufe masa sutudiyo.
Ya cigaba da cewa:
"Bayan samun korafin, an tura masa takardar gayyata sau biyar amma bai taho caji ofis ba. An kuma tura masa wasika ta hannun mahaifinsa amma bai zo ba.
"Rundunar yan sanda ba ta son rushewar doka da oda shi yasa aka so kama shi ranar Talata yanzu kuma ya fara sakin bidiyo, yana fadan abubuwa. Mahaifinsa na roko amma fada masa idan bai kawo kansa daga yanzu zuwa Juma'a ba, za mu kama shi."
A baya, rundunar yan sandan ta jihar Ogun ta taba umurtar Portable ya kai kansa ofishinsu mafi kusa.
An umurci ya kai kansa ne saboda zargin duka da aka ce ya yi wa wani tsohon DJ dinsa mai suna DJ Chicken.
Asali: Legit.ng