Bidiyo: 'Dan Najeriya yayi Wuff da 'yar Indiya, Yace Babban Burinsa ya Cika a Rayuwa
- Wani biki mai kayatarwa na wani 'dan Najeriya da masoyiyarsa 'yar Indiya ya kayatar da masu amfani da yanar gizo
- Kamar a shirin fina-finan kasashen ketare, masoyan sun shiga daga ciki a wani taro da suka yi mai kayatarwa a al'adar turawa
- Wasu masu amfani da soshiyal midiya sun yi mamakin yadda masoyan basu duba bambancin da ke tsakaninsu ba, suka yi murnar aurensu
Bidiyon bikin auren wani mutumi 'dan Najeriya da masoyiyarsa 'yar Indiya ya yi tashe a soshiyal midiya na dandalin TikTok.
Faifan bidiyon da @grakeshotz a kafar ya wallafa ya tattara sama da jinjina 600 yayin da masoyan suka matukar kayatar da masu amfani da yanar gizo.
Sanye ka suturun Indiyawa, aka daura auren masoyan kamar a shirin fina-finan kasashen ketare.
Amaryar ta sanya sarkar kai kirar zinare, wacce ta zubo zuwa fuskarta da tafin hannayenta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
'Yan soshiyal midiya sun bayyana ra'ayoyinsu game da bikin auren.
Martanin jama'a
Senyonjo Denismaaso ya ce:
"Kadan da kadan duniya zata koma babban wurin so." Neemart ta ce: "Ina tayaku murna da rayuwa mai dadi. "Ubangiji wannan shi ne abun da nake rokonka."
Lovely boy ya ce:
"Soyayya ♥️natsuwa ce✌️wannan shi ne muke bukata a duniyar nan."
uset2744256581533 ya ce:
"Kai wannan abun ban sha'awa ne. "Ina tayaku murna."
FEEZA ya ce:
"Ta yiwu sun matukar shan wahalar kai wa wannan ranar♥️♥️Ina tayaku murna da fatan alheri."
vendettalady5 ta ce:
"Kun kayatar, ya kamata mu hada kanmu tun duk din mu 'yan adam ne♥️yana da kyau a nuna wa duniya soyayya bata dubi da kala. Nasa muku albarka duka."
Keburan talauci: Matashi ya bukaci a bashi duka sadakar da yayi a coci
Bidiyon Budurwa Tana Murna Bayan Saurayinta Ya Kai ta SIyan Gwanjo Kafin Zuwa Ranar Masoya ta Duniya
A wani labari na daban, wani matashi 'dan Najeriya ya yi kira ga cocin Dunamis da ta biya shi dukkan sadakar da ya taba zuba mata.
Yace talauci ya saka shi gaba kuma bashi da cin yau balle na gobe. a cewarsa ya hakura da aljanna baki daya.
Matashin yace a kirge yake da yawan kudin da ya zuba na sadaka, don haka a bashi kayan shi kawai a zauna lafiya.
Asali: Legit.ng