Ku Dawo Min da Sadakata, Bana Son Aljannar: Matashi ya Caccaki Cocinsa

Ku Dawo Min da Sadakata, Bana Son Aljannar: Matashi ya Caccaki Cocinsa

  • Wani mutumi 'dan Najeriya ya bukaci Majami'ar Dunamis International Gospel da su tattaro masa kan dukiyarsa da ya bayar a matsayin sadaka
  • Mutumin mai suna Maazi Chukwudiaso Onyema ya ce bai damu da shiga aljanna ba yafi so ya shiga wuta
  • Onyema, wanda ya yi ikirarin an hure masa kunne, ya kara da cewa yana kirge da kudin sadakar da ya ba majami'ar

Wani mutumi 'dan Najeriya ya ce ya riga ya yanke shawarar shiga wuta maimakon aljanna kamar yadda a da ya tsara.

Keburan talauci
Ku Dawo Min da Sadakata, Bana Son Aljannar: Matashi ya Caccaki Cocinsa. Hoto daga TikTok/ambassadortv, @chikakaty1 Facebook/Paul Enenche, and Bloomberg/Getty Images.
Asali: UGC

Daga karshe dai, Mutumin mai suna Maazi Chukwudiaso Onyema ya bayyana a wani bidiyo yana kira ga Majami'ar Dunamis International Gospel da ta maido masa duk sadakar da ya dauki tsawon shekaru yana bada wa a majami'ar.

Onyema ya kara da bayyana yadda yake amsar keburan talauci wajen daukar ragamar iyalinsa.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Tona Abin da Ya Jawo Manya Suke Adawa da Tsarin Canza Nairori

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin nuna katin sadakarsa, Onyema ya ce baya cikin hayyacinsa lokacin da ya yi ta bada sadakar a majami'ar, inda ya yi ikirarin an hure masa kunne ne.

Onyema ya ce a halin yanzu yana amsar keburan talauci, kuma yana kirge da duk kudin da ya bayar na sadaka a katin sadakarsa kuma yana so a maido masa da shi gaba daya.

A cewarsa, ba ya bukatar duk wata kyauta da kyautatawa da ya yi wa majami'ar.

Ya kara da cewa, ya fara zuwa majami'ar Dunamis a 2008, inda suka shawarcesa da ya tara dukiya ga kansa a aljanna ta hanyar tara sadaka.

A bidiyon TikTok din da ya ke tashe, Onyema ya nuna shaidar takardun da ya samu bayan horarwan da majami'ar da ya yi.

Kamar yadda ya ce, yunwa na fafarar cikinsa ga tsananin wahala a bankinsa cikin rashin sa'a garesa saboda halin rashin kudi da Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

Kai Mummuna Ne: Budurwa Ta Kunyata Saurayi, Ta Ki Amincewa Ta Aure Shi, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

'Yan Najeriyan da ke TikTok su na kan yin tsokaci ga bidiyon da @chikakaty1 ta wallafa. Wanda tun Ambassador TV suka fara wallafa wa.

@Temidayi Femi ya ce:

"Babu wanda ya tilasta maka bada kudinka mana. Wannan Najeriyar na da ban dariya. Gaisuwa daga dakin dukiya aljanna.

@maryolatunji701 ta ce:

"Maganar gaskiya ita ce idan kana cikin matsala wasu majami'oin basa nuna damuwa. Ina rokon Ubangiji ya bada mamaki."

@NazzyC ya ce:

"Nayi Imani faston zai ga wannan don taimakawa saboda babu abun da yafi ban takaici da ba zai jawo ba. Mutum mai jin yunwa na cikin bacin rai."

Budurwa ta cika da murna bayan saurayi ya kai ta siyan gwanjo

A wani labari na daban, wata budurwa ta fada murna a bidiyo bayan saurayinta ya kai ta siyan gwanjo domin zagayowar ranar masoya.

Ya bata zabi inda yace ta zaba tare da darje kayan da ta ke so, wannan lamarin ya ja mata yabo mai tarin yawa daga jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng