Budurwa Tayi Watsi da Saurayinta Bayan ta Kammala Digiri, Tace ba Ajinsu Daya ba

Budurwa Tayi Watsi da Saurayinta Bayan ta Kammala Digiri, Tace ba Ajinsu Daya ba

  • Wata budurwa da ta kammala digirinta na farko a kwaleji tayi watsi da saurayinta, inda tace ta wuce da ajinsa ba ta ga dalilin cigaba da alaka da shi ba
  • Budurwar ta bayyana hakan ne a dandalin Twitter a shafinta @_RaaayT, gami da cewa mutune basu isa su taimakawa wanda bashi da burin taimakon kansa ba
  • Ta kara da bayyana yadda tsawon lokaci saurayin nata bai da burin kaiwa wani mataki da ya wuce wanda yake a yanzu, hakan yasa ta raba gari da shi

Wata budurwa ta shaidawa soshiyal midiya yadda tayi watsi da saurayinta bayan gama kwaleji.

Budurwa
Budurwa Tayi Watsi da Saurayinta Bayan ta Kammala Digiri, Tace ba Ajinsu Daya ba. Hoto daga @RaaayT
Asali: Twitter

Ta shaida hakan ne a shafinta na Twitter @_RaaayT gami da bayyana dalilin kawo karshen alakar tasu saboda ta wuce da ajinsa.

A cewar matar, shi ba mai son dagawa daga matakin da yake bane ko kawo cigaba ga kansa saboda haka ta raba gari da shi bayan kammala digirinta na farko.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Auri Mai Nakasu Bayan Ta Rabu Da Attajirin Saurayinta

A cewarta, daga gani babu bukatar su cigaba da zama guri daya fiye da makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Ray, ba ta bayyana ko shi din ya bar makaranta bane, bai da ilimi ko kuma bai da fasahar aiki.

Ta rubuta a Twitter cewa:

”Ban dade da gama kwaleji ba, sai dai na gane gayen ba aji na bane kuma ba ya kokarin ganin ya kai.
”Ba za ka iya taimakawa mutanen da basa kokarin taimakon kansu ba. Yanzu na farka daga nannauyan bacci bayan samun kwalin digiri, babu bukatar cigaba da mu'amala da shi."

Mata sau da yawa shekar soyayyarsu kan canza idan suka samu canjin rayuwa. Suna kara buri da fatan su samu namijin da ajinsu zai zama daya da irin cigaban da suka samu.

Wannan lamarin kuwa yana matukar firgita zukatan maza inda hakan ke sa su yi wa mata kudin goro kan cin amanar kauna da soyayya.

Kara karanta wannan

Ko da ne ga dan siyasa: Bidiyon mahaukaciyar da ta haifi jariri a kasuwa ya bar baya da kura

Bidiyon Obasanjo Zanzare cikin kayan makaranta, Yana aikin manyan firifet

A wani labari na daban, bidiyon tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo sanye da kayan makarantar sakandare da ya halarta ya birge.

A bidiyon, an gan shi yana saka tsawa tare da gyarawa na kasa da shi zama duk a cikin aikin manyan firifet.

Asali: Legit.ng

Online view pixel