"Wa Ya Aike Shi": Bidiyon Ango Ya Fadi Kasa Yayin Kokarin Daukar Matarsa Yayin Da Suke Rawa A Ranar Aurensu
- Ba sabon abu bane dai amarya da ango su girgije su dan taka rawa musamman a ranar aurensu don nishadantarwa
- Sai dai a wannan karon wani ango bai tsaya ga rawar ba kawai ya nemi ya dauki matarsa caras da hannu ya daga ta sama
- Amma, akasin yadda ya so, bai yi nasarar daukan matarsan ba a hannu sai dai dukkansu suka fadi kasa warwas, mutane suka taso suka taimaka musu
Wani bidiyo ya fito a shafukan sada zumunta inda wani ango ya fadi kasa warwas yayin bikin aurensu.
Angon ya fadi kasa ne a yayin da ya ke kokarin daga amaryarsa a wurin bikin aurensu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amarya da angon suna rawa ne irin ta masoya kuma a matsayinsu na mata da miji sai a yayin da baki da aka gayyata ke kallonsu.
Daga bisani, angon ya yanke shawarar yana son ya daga dauki amaryarsa da hannu ya daga ta sama.
Sai dai ba yadda ya shirya abin ya faru ba domin sun fadi kasa tare ta danne shi.
Daga nan sai mutane da suka halarci bikin auren suka taso suka taimaka wa amaryar ta tashi tsaye.
Shima angon daga bisani ya tashi ya nemi su cigaba da rawar amma dai mutane da suka zagaye amaryar suna cigaba da duba ta don tabbatar lafiyarta kalau.
Ga bidiyon a kasa:
Wasu masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani
@CryptoDefLord ya ce:
"Ka auri abin da za ka iya dauka amma ba za su ji ba. Yanzu ga sakamakon nan."
@Christi10714431 ta ce:
"Burkutu ne ta bashi kwarin gwiwa idan ba haka ba mai zai sa ya yi tunanin zai iya daukan wannan yar duma-duman, rigarsa ya kusa fita daga jikinsa."
@MkpeAbang ya ce:
"Yawan kallon zeeworld ne ya janyo masa. Kamata ya yi ya tafi gidan motsa jiki kafin auren. Ya bari yan kauyensu sun yi nasara a kansa."
@VictoryIkenna:
"Komai na tafi dai-dai kafin ya kauce daga kan hanya."
@Concerned_Igbos1 ya ce:
"A lokacin da ka yanke shawarar kunyata kanka don birge MC, MC da ya biya ya yi aikinsa."
@Greatman450 ya ce:
"Kana nufin, ba ku gwada yi ba a baya kafin ku fito fili ku yi wannan."
Asali: Legit.ng