Bidiyon Lokacin Da Gwamnan APC Ya Cire Gilashi Don Kallon Ƴan Mata Da Ke Tiƙa Rawa 'Zigidir' A Calabar

Bidiyon Lokacin Da Gwamnan APC Ya Cire Gilashi Don Kallon Ƴan Mata Da Ke Tiƙa Rawa 'Zigidir' A Calabar

  • Masu amfani da soshiyal midiya suna ta ragargazan Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers bayan wani bidiyonsa ya bazu
  • A cikin bidiyon da ya bazu an ga Gwamna Ayade yana kallon yan mata suna rawan gargajiya 'zigidir' a bikin Calabar International Festival 2022
  • Yayin da ya ke kallon, an hangi ya cire gilashinsa kuma hakan ne ya sa mutane ke ta magana kan bidiyon

Cross River, Calabar - Ana ta maganganu kan Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers biyo bayan wani bidiyonsa a wurin bikin Calabar International Festival na 2022 da ya bazu.

An hangi jigon na jam'iyyar APC a bidiyon da ya bazu yana kallon yan mata 'zigidir' suna rawan gargajiya a wani wurin da ya yi kama da filin wasanni na U.J. Esuene, a Calabar.

Kara karanta wannan

2023: A Karshe, Atiku, PDP Sun Samu Sako Mai Karfafa Zuciya Daga Gwamnonin G5

Gwamna Ben Ayade
Lokacin Da Gwamnan APC Ya Cire Gilashi Don Yi Wa Zuka-Zukan Yan Mata Da Ke Rawa 'Zigidir' Kallo Mai Kyau. Hoto: Sir Benedict Ayade CON
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma, abin da Gwamna Ayade ya aikata yayin da ya hangi yan matan na cashewa ne ya janyo maganganu a soshiyal midiya.

Gwamnan wanda ya saka hula beret mai launin ruwan kwai da riga yana cire gilashinsa domin ya kalli yan matan da ke rawan sosai a wani sashi na filin wasannin.

Masu amfani da soshiyal midiya sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi

Yayin martani kan lamarin, wasu yan Najeriya sun tafi Twitter don bayyana ra'ayinsu kan abin da ya faru a filin wasannin na U.J. Esuene.

Idoje Clement yayin tsokaci kan lamarin ya kare gwamnan na jihar Cross Rivers yana mai cewa:

"Rawar yan Ghana a bikin Calabar International Festival 2022... matarsa na zaune kusa da shi. Ya cire gilashinsa ne don ya goge zufa daga idonsa!"

@macquad ya ce:

"Da kyau, wato sun yi rawa zigidir a Calabar Carnival, ban ga irin hakan ba shekarun baya...Shin wannan cigaba ne ko ci baya? Nuna cinya kawai yasa aka hana mu rawa a gasar CDS na rawa da dirama a Abuja wancan shekarar."

Kara karanta wannan

Na Sha Wahalar Kawai: Magidanci Ya Gane Dukkan Yaran da Matarsa ta Haifa ba Nashi Bane

@irikefe_ogaga zo ka duba wannan."

Sunny Chukwu ya ce ba wani babban abu bane domin al'ada ce na mutane kamar kasar Swaziland.

Ya ce:

"Bikin rawa na Swaziland! Ana yi kowanne shekara inda yan mata da aka ce ba su san maza ba ke rawa 'zigidir' don sarki ya zabi sabuwar mata."

Asali: Legit.ng

Online view pixel