Bidiyon Yadda Fasinjoji Suka Farfasa Mota Bayan Direba ya Arce da Kudinsu
- An yi karamar dirama da ta hada da direban bas da fasinjoji kan kudin motarsu da ya kai jimillar sama da dubu talatin
- Direban bas din ya yi karyar lalacewar bas din kuma ya tsere da kudaden fasinjoji tare da barinsu a tsaye
- Fusatar kan yadda direban yayi musu, yasa fasinjojin suka dauka doka a hannunsu inda suka fara balle sassan motar don fanshewa
Legas - Fasinjojin da suka hau wata motar haya a jihar Legas sun babbale sassan motar duk a kokarinsu na siyar da ita don fanshe kudinsu da direba ya arce da su.
Daya daga cikin fasinjojin, wacce budurwa ce ta nadi bidiyon tare da yada shi a TikTok inda ta sanar da abinda ya faru a Legas.
Kamar yadda budurwar tace, halayyar rashin hankalin fasinjojin ta faru ne sakamakon muguntar da direban motar yayi musu.
Ta rubuta cewa, direban bas din yayi kamar motar ta samu matsala amma ya tsere da kudin motar fasinjojin da ya zarce N30,000.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An ga fasinjojin suna cire kujerar direban, kayan shi da wasu muhimman abubuwan da zasu iya dauka.
Wasu sun cire batirin motar da niyyar siyar da shi.
Kalla bidiyon a kasa:
Soshiyal midiya
Iser852626738383627 yace:
“Matsalar ta shafi jama’ar ne ba wai inda suke ba shiyasa zasu bada gudumawa duk inda suke da yawa.”
Andrew Bennison yace:
“Na kosa ‘yan Najeriya masu yawa su zo rayuwa a kasa ta! Kowacce rana za mu iya samu wannan nishadin.”
John Doe yace:
“A kasa ta direban tasi ya yi karyar cewa batirinsa ya mutu sai yace fasinjoji su tura masa motar. Cinka wanda ya tafka asara.”
Matt yace:
“Wannan daidai yake da £55, wannan har ya kai ga ya tsere dasu tare da rasa aikinsa? Tambaya mai amfani.”
Annoyedhuman25 tace:
“Ina tayar, sitiyari, injin din motar da? Ku siyar da dukkan sassan ku cafke kudin ku, canjin ku siya tsire.”
Amaka tace:
“A gaskiya na tsorata da Legas. Ina don zuwa can amma na san bai dace in je ba.”
Bidiyon babur mai tashi sama ya bayyana
A wani labari na daban, rahoton Reuters ya bayyana bidiyon wani babur mai ban mamaki wanda aka kera yana tashi sama.
Babur din shi ne na farko a duniya dake tashi sama kacokan din shi.
Asali: Legit.ng