Bayan Shekaru 2 da Soyayya ta Watse Tsakaninta da Saurayinta, Ta kwace Motar da Bashi Kyauta

Bayan Shekaru 2 da Soyayya ta Watse Tsakaninta da Saurayinta, Ta kwace Motar da Bashi Kyauta

  • Wata kyakyawar budurwa ta wallafa irin kazaman abubuwan da ta gani a motar da ta ba saurayinta lokacin da suna soyayya
  • Hakan ya biyo bayan rabuwarsu shekaru biyu da suka shude, har ta kai ga budurwar ta kwace motar da tabawa tsohon saurayin nata daga bayan
  • Matar mai matukar kirki ta kara da bayyana dalilin da yasa ta bar motar tsawon shekaru biyu a hannunsa kafin ta nemi ya maido mata da abun ta

Wata budurwa ta tada kura a dandalin soshiyal midiya na TikTok bayan wallafa irin tarkacen da ta gani a motarta da ta dade a hannun tsohon saurayinta.

Ta wani shafin TikTok @diahy.fox, ta nuna yadda cikin motar ya kasance, wanda ke nuna yadda hunhuna ke cigaba da rayuwa a wurare daban-daban a ciki.

Budurwa da saurayin
Bayan Shekaru 2 da Soyayya ta Watse Tsakaninta da Saurayinta, Ta kwace Motar da Bashi Kyauta. Hoto daga TikTok/@dishy.fox
Asali: UGC

Sauran bidiyon da ta dauka sun nuna yadda motar ta fito fes wacce ta bayyana yadda aka dauki tsawon awanni uku ana kankarewa gami da wankewa.

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Gano Mijinta Ya Yi Amarya a Ɓoye Har Sun Haihu, Ta Je Gidan An Buga Dirama a Bidiyo

"Se da na dauki tsawon awanni uku wajen kwashe dattin motar."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Tace.

An tambayeta dalilin barin motar na shekaru 2

Yayin da masu amfani da yanar gizo suka tambayi dalilin da yasa ta dauki tsawon lokaci kafin amsar motarta, ta sake yin wani bidiyo inda ta bayyana:

"Muna tare lokacin da motarsa ta lalace. Kawai nayi kokarin nuna masa mutuntaka ne, budurwa mai kima... Na taimakesa.
"Kun san idan kana son mutum za ka yi iya kokari don taimaka masa. Amma bayan mun rabu, ba naso in yi harkar karanta ko in kuntatawa rayuwarsa. Duk da haka ina so ya samu aiki sannan yayi rayuwa mai dadi.
"Hakan ne dalilin da yasa yayi amfani da ita tsawon shekara bayan mun rabu.."

Martanin jama'a

Relichunter37814 ta ce:

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Garzayo Najeriya Daga Turai Domin Haduwa Da Sahibinta, Bidiyonsu Ya Yadu

"Za ki iya bincikar dalilin da yasa ta zama haka, amma za ki iya maka shi kotu gami da bukatar wasu kudi."

Sarah ta ce:

"Rai na gaba daya ya baci kuma na daburce. Yadda na gyara motar har tayi kyalli gami da wallafa ta."

Wind S ya ce:

"Yarinya, ki fada min baki biyan inshoran wannan? Idan da ni ne ai da na kira su nace tsohon saurayina ya sace min mota."

sav ya ce:

"Wannan ai abun kunya ne gare shi, wai me ma yake yi ne."

Isaac Pando ya ce:

"A matsayina na wanda ya duba motar da kyau, zan ji kamar ana tsingulina idan na fara amfani da motar. Ki kai ta wajen kwararre, na miki alkawari kashi 99.9 na barnat zai tafi."

Budurwa ta bar saurayi ya kwanat jikinta a Bas

A wani labari na daban, budurwa ta bar saurayi ya kwanta a jikinta yayin da suka shiga mota tare.

Ta wallafa hoton inda tace bai tambayeta kudi ba kuma ya birgeta saboda jikinta kawai ya kwanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng