Matan tsohon fitaccen mawaki Eedris Abdulkareem zata bashi kodanta

Matan tsohon fitaccen mawaki Eedris Abdulkareem zata bashi kodanta

  • Matan tsohon fitaccen mawakin Najeriya Eedris Abdulkareem zata taimaka masa da kodanta saboda lalurar koda da yake fama dashi
  • Mawaki MI Abaga ya yi kira ga magoya bayan Eedris da masu hannu da shuni da su taimaka masa da kudin da za a yi masa tiyatar dashen koda
  • Ana sa ran za a yiwa Eedris Abdulkareem dashen koda a karshen watan Yuli

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Legas - Wani na kusa da iyalan mawaki Eedris Abdulkareem ya shaida wa jaridar TheCable Lifestyle cewa matar mawakin ta dauki nauyin ba wa mijinta kodarta bayan an kammala yi masa dukkan nau'ikan gwaje-gwaje.

Abdulkareem, tsohon shahararren mawakin Najeriya, yana fama da ciwon koda.

Ana dai yi wa mawakin wankin koda a wani asibiti da ke Jihar Legas kuma ana sa ran za a yi masa dashen koda ne a karshen watan Yuli.

Kara karanta wannan

Ya kamata ka girmi siyasar kabilanci: Peter Obi ya caccaki Kwankwaso

IDRIS
Matan mawaki tsohon fitaccen mawaki Eedris Abdulkareem zata bashi kodanta; FOTO THE CABLE
“Matar zata ba shi gudummawar kodarta. Abin da ya rage a yanzu shi ne a samu adadin kudin da ake bukata don yi masa aikin tiyata,” in ji shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shahararren mawakin gambara MI Abaga, ya yi kira ga magoya bayansa da masu hannu da shuni da su taimakawa mawaki da kudi dan a samu anyi masa aikin tiyatar cutar da yake fama dashi.

MI ya kuma bayyana cewa "mun samu mai bada gudummawar koda a cikin danginsa".

Zargin safarar sassan Jiki : Ike Ekweremadu Ya Koma Kotu

Burtaniya - Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya koma Kotun Majistare na kasar Burtaniya domin ci gaba da shari’ar sa. Rahoton Channels Tv

Rundunar ‘yan sandan Birtaniya ta kama Ekweremadu da matarsa, Beatrice a ranar 23 ga watan Yuni bisa zargin safarar mutane da kuma girbin sassan jikinsu da suka saba wa dokar bautar zamani ta kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa