Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

  • Naziru M. Ahmed wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya fito shafinsa na Facebook, yana sukar masu sana’ar wasan kwaikwayo, yana kare Almajirai
  • Da yake magana a Facebook a ranar Juma’a, 22 ga watan Afrilu 2022, Sarkin Waka ya fadi abin da ya kira da gaskiyar da ba dole tayi wa kowa dadi ba
  • A kokarinsa na kare Almajirai, ya nuna babu manyan Almajirai irin ‘yan wasan fim domin su ne asalin mutanen da iyayensu suka fita daga harkarsu

Kano - Shahararren mawakin nan, Naziru M. Ahmed ya yi rubutu, yana cewa almajiranci da iyaye suke aika yara ya na da amfani, kuma sun ci moriyar hakan.

Sarkin Waka ya ce tura yara karatu da iyaye suke yi, ya fi a kan a kyale su da makamai a cikin jeji.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

"Wannan shine gaskiya malamai. Ko tayi dadi, ko kar tayi dadi. Kowa ya dauko sharrinsa sai kan almajirai da iyayensu??
To mu munsan abin da kuke kira da almajirci duk da ba sunansa kenan ba, mun san niyyar da ke sa iyaye su kai ‘ya ‘yansu, mun kuma ga amfaninsa.
Watau kun fi so a bar yara a daji babu manufa ayi ta ba su bindigu suna kashe mu? Wannan shine burinku??"

A karshe sai ya kare maganarsa da cewa:

“Wannan shine kawai. Ayi hakuri damu!”

Masu karatu ba Almajirai ba ne

Daga nan kuma sai mawakin ya daura wani hoto da yake sukar ‘yan wasan kwaikwayo, ana cewa taurarin fim ne wadanda iyayen suka ce, su je su karata.

Ga abin da hoton yake cewa:

Kara karanta wannan

Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur

“Ba Almajirai ne ‘ya ‘yan da iyayensu suka haifa, su ka kasa kula da su ba. Idan ka na neman ‘ya ‘yan da iyayensu suka haifa, kuma su ka kasa kula da su, to ka taho masana’antar fim.”
Naziru Sarkin Waka
Naziru Sarkin Waka Hoto: @sarkinwakah
Asali: Instagram

Martanin mutane a Facebook

Amma mutane su na ta maida masa martani a kan wannan. Wasu sun goyi bayan mawakin, wasu kuma su na ganin akwai gyara a abin da ya ke fada.

Wato ƙasarnan idan Kanada kuɗi duk abinda kaga dama zaka iya faɗa yanzu wannan maganar inda talaka ne ya faɗeta wlh gidan yari zai kwana.

– Deeny Shamsuddeen

Sarki ka jijjige tebur Wallahi

– Auwal Shariff Abubakar

Wannan magana cike take da son rai. Kowa yasan wannan ba gaskiya bane.

- Yamai Muhammed

Sarki, ka kira ruwa.

– Musa Shehu

Gaskiya ka. Su sun san yadda za su hana duk wannan abin, amma saboda zalunci ba zasu hana ba. Bara da maular yara za a hana, ba yin hijira (almajiranci) zuwa wani gari ba don neman ilimi. – Abubakar Sirdeeq Yushau

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Abin da ya sa aka ga Buhari ya yafewa tsofaffin Gwamnonin da ke kurkuku

Tofa!!! Wata sabuwa. Gaskiya ne Sarki, a fada musu ita ko ba su so. Allah yaja kwana da arziki Mai albarka. Ya kuma kara maka basira bijahi sayyidina ya rasulullah. S.A.W. Amen

– Muneer Usman

Kwamared Naziru kai ma fa dan fim ne, Aminu Saira ‘dan fim ne, Misbahu uba ne a harkar fim. Kaf gidan ku ba a san ku a komai ba bayan nanaye. Wannan abin da kakeyi kamar kan a dabawa kanka wuka ne ba ka gane ba, tun da Nafisa ta fita labarina ku ka tsaneta, kuma Mahmud yace biya ne ba ku yi sosai. So wannan fadan ku ne na cikin gida, ku ‘yan fim. Dan haka can ga su gada.

- Malam Abdu GCFR

Allah ya kiyyaye

– Abdulbarri Busari

Da Kyau Sarki! Wannan wani Saƙo ne Dunƙule. Akanka, Abokan Sanaar ka, da duk Masu Ihun Zagin Almajirai (Makaranta Qur'ani). Ko Addininka da GidanKa yayi Umarnin ka Fara Gyara Kafin ka Tafi waje.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

- Al Murshid

Sarki zasu kara haurowa kan ka, su ma rubdugu.

- Mudassir Ali Bamanga

Allah dai Ya ma albarka Sarki

- Sada Sulaiman Usman

Ai yanzu almajiri ne babban employer kuma influencer a Kannywood. Shi ke basu kudi da motoci da gidaje kuma shine jagoran su a 13-13.

- Isa Mansur

A makon nan ne kuma aka ji tauraron yana sukar APC a kan tsadar kudin fam din shiga takara, ya ce jam’iyyar ba ta talaka ko mai karamin karfi ba ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng