Dan takara a 2023: Gwamnan APC ya ce Buhari ne zai zabi yankin da zai kawo dan takara
- Wani gwamnan APC ya bayyana yadda jam'iyyar za ta bi wajen tsayar da dan takarar shugaban kasa na gaba
- Wannan na zuwa ne daga bakin gwamnan jihar Ogun yayin da ya ziyarci shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja
- Ya bayyana cewa, shugaban kasa ne ke da ta cewa kan wanda ya dace jam'iyyar ta tsayar a wannan fanni
Abuja - A yayin da jam’iyyar APC ke shirin gudanar da taron gangaminta na kasa a watan Fabrairu, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne zai ba da jagoranci domin taimakawa kan zaban yankin da zai kawo dan takara.
Gwamnan wanda ya jagoranci wata kakkarfar tawaga ta wasu shugabannin jihar a ziyarar godiyar da suka kai wa shugaban kasa a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a, ya ce Buhari ne zai ci gaba da ba da alkiblar ciyar da jam’iyyar gaba.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, ya ce shi ba shi da hurumin bai wa jam’iyyar APC shawara kan fito da shugaba daga wata shiyya a matsayinsa na gwamna, Tribune ta ruwaito.
Hakazalika, ya ce amma jam’iyyar na aiki kan tsarin, wanda ya ce za a sanar da mafita bayan majalisar zartarwar jam'iyyar ta APC ta yanke shawari.
A cewarsa, bayan amincewar majalisar ne za a san daga ina aka yanke jam'iyyar ta fito da shugaban kasa na gaba, kamar yadda TheCable ta ruwaito.
Abiodun ya ce tawagar ta je Villa ne domin gode wa shugaban kasa bisa ziyarar da ya kai jihar kwanan nan domin kaddamar da ayyuka da dama.
Tare da shi akwai tsohon gwamnan jihar, Olusegun Osoba; Shugaban Majalisar sarakunan gargajiya, Oba Babatunde Ajayi; tsohon mataimakin gwamna, Alhaja Salimot Badru, da kuma babban dan kasuwa, Cif Sulaiman Adegunwa.
Yadda zan bi wajen shawo kan rigingimun jam’iyya idan na zama Shugaban APC inji Sanata
A wani labarin, daya daga cikin manyan masu neman takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa, Sanata Sani Musa ya yi alkawarin magance rigingimun cikin gida.
A ranar Alhamis, 27 ga watan Junairu 2022, Vanguard ta rahoto Sanata Sani Musa yana cewa zai gyara APC idan har ya yi nasarar zama shugaban jam’iyya.
Da yake hira da gidan talabijin na Channels a wani shirin siyasa a yammacin Larabar nan, Sani Musa ya shaidawa Duniya manufarsa da ya yi wa lakabi da 3R.
Asali: Legit.ng