Harin jiragen saman NAF a Kukawa, jihar Borno, ya hallaka fararen hula ciki har da masunta da direbobi, yayin da ake binciken sahihancin bayanan sirri.
Harin jiragen saman NAF a Kukawa, jihar Borno, ya hallaka fararen hula ciki har da masunta da direbobi, yayin da ake binciken sahihancin bayanan sirri.
Babban bankin Najeriya watau CBN ya karbe lasisin da ya bai wa wasu bankuna biyu na ajiya da rance, Aso Savings and Loans Plc da Union Homes Savings and Loans Plc
Wani matashi da ya arce da wata mota ta naira miliyan 55 a kwanakin baya a Abuja, ya bayyana cewa ba da nufin sata ya dauki motar ba. Ya ce kawai dai ya tafi.
Wani magidanci a birnin tarayya Abuja, Raphael Chima, ya nemi Kotun kwastumare mai zama a birnin tarayya ra raba aurensa da Joy saboda bata kaunar zaman lafiya.
An kama wani matashi da ake zargin ya shake wuyan mahaifiyarsa har lahira a karamar hukumar Ijebu-Ode da ke jihar Ogun, an tabbatar cewa matashin na shan kwaya.
Biyo bayan sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar 1 ga watan Muharram na shekarar 1445, jihohi irin su Sokoto, Ƙebbi, Osun duk sun bada hutu.
Gwamnna jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, a matsayin ranar hutu a jihar domin murnar zagayowar shekarar musulinci.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya janye batun raba N8000 a wata, dole za a sake duba tsarin da ya yi niyyar kawowa domin rage radadin janye tallafin fetur.
Jam'iyyar Labour Party ta bayyana cewa yanzu ƴan Najeriya suka soma indai shan wuya ne a ƙarƙashin gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a ƙasa.
A daren ranar Lahadi, Babagana Umara Zulum ya kai ziyara zuwa asibitin gwamnatin Gwoza a lokacin da mutane ke barci, ya iske wurin babu wutar lantarki a lokacin
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana ranar Laraba, a matsayin ranar hutu saboda murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.
Labarai
Samu kari