Kotu Ta Sanya Lokacin Yanke Hukunci kan Bukatar Belin El Rufai
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai na ci gaba da zuwa kotu kan tuhume-tuhumen da hukumar ICPC ke yi masa
- El-Rufai ya musanta sababbin tuhume-tuhume tara da ICPC ta shigar a kansa, yayin da ya nemi kotu da ta ba da belinsa
- Alkalin kotu ya dage sauraron bukatar belin da tsohon gwamnan ya gabata a zaman da aka yi a ranar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Babban kotun jihar Kaduna ta yi matsaya kan bukatar neman beli da Nasir Ahmad El-Rufai ya gabatar a gabanta.
Babbar kotu ta ɗage saurarar buƙatar neman belin da tsohon gwamnan na jhar Kaduna ya shigar, zuwa ranar 14 ga watan Afrilu, 2026.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa alkalin kotun ne ya yanke hakan a ranar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026.
El-Rufai ya bayyana a gaban kotun ne ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, yayin da ake ci gaba da shari'ar da hukumar ICPC ta shigar kansa tare da Amadu Sule, kan zargin almundahanar kuɗaɗe da cin zarafin ofis.
El-Rufai ya musanta tuhume-tuhumen ICPC
Yayin zaman kotun, El-Rufai ya musanta laifuffuka guda tara da ICPC ta karanta masa, waɗanda aka shigar tun a ranar 18 ga Maris, 2026.
A ɓangare guda, hukumar ICPC ta buƙaci kotu da ta cire sunan wanda ake ƙara na biyu, Amadu Sule, daga cikin tuhumar tare da janye dukkan zargin da ake masa, inda alƙalin ya amince da wannan buƙatar.
Malam El-Rufai ya nemi beli a kotu
Jaridar the Punch ta ce lauyan El-Rufai, Ukpon Akpan, ya roƙi kotun da ta ba wa wanda yake karewa beli, inda ya bayar da hujjar cewa tsohon gwamnan ba zai gudu ba kuma a shirye yake ya bi dukkan sharuɗɗan da kotu za ta gindaya masa.
Sai dai masu shigar da ƙara (ICPC) sun nuna rashin amincewarsu da buƙatar belin, suna masu cewa laifuffukan da ake zarginsa da su suna buƙatar nazari mai zurfi na shari’a.

Kara karanta wannan
APC: Tsohon saƙon shugaban INEC ya jawo zazzafar muhawara kan sahihancin zaben 2027
Kotu ta ki ba da belin El-Rufai
Bayan sauraren hujjojin ɓangarorin biyu, mai shari'a, Darius Khobo, ya ƙi bayar da hukunci nan take, maimakon haka ya ɗage shari'ar zuwa ranar 14 ga Afrilu (gobe) domin ci gaba da saurarar ƙarar da kuma yanke shawara kan buƙatar belin.
Lauyan tsohon gwamnan, Ukpon Akpan ya bayyana cewa:
"Kotu ta saurari buƙatar beli kuma wanda ake ƙara ya musanta laifuffukan. Masu shigar da ƙara sun gyara takardar tuhumar inda suka cire mutum ɗaya, suka bar Mallam El-Rufai shi kaɗai."
Lauyan ya ƙara da cewa an ba su takardar sababbin tuhumar ne a safiyar ranar Litinin ɗin nan a cikin kotu, shi ya sa ba su iya ci gaba da saurarar ƙarar ba gaba ɗaya.
“Tuhume-tuhumen sababbi ne, don haka duk abin da muka gani, za mu yi nazari a kansu mu gudanar da bincikenmu, sannan mu sanar da duniya. A yanzu ba abin da za mu iya yi game da tuhumar; sababbi ne fil."
“An ba mu su ne muna cikin kotu. A yanzu dai, El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun ICPC."
- Ukpon Akpan

Source: Twitter
El-Rufai ya kai korafi gaban babbar alkali
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kai ƙorafi ga babbar Alƙaliyar Najeriya (CJN), Kudirat Kekere-Ekun.
Tsohon gwamnan na Kaduna ya shigar da korafin ne yana neman a sauya Alkalin da ke jagorantar shari’ar da ake masa.
El-Rufai ya buƙaci a cire mai shari'a R. M. Aikawa daga shari’ar, tare da miƙa ta ga wani Alƙali a sashen kotun Kaduna ko kuma wani wuri daban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

