Wata Sabuwa: Matsalar da Aka Samu a Sulhun Amurka da Iran Ya Rusa Burin 'Yan Najeriya

Wata Sabuwa: Matsalar da Aka Samu a Sulhun Amurka da Iran Ya Rusa Burin 'Yan Najeriya

  • Farashin danyen mai na iya kara tsada matukar Amurka da kasar Iran suka ci gaba da yaki bayan karewar yarjerniyar tsagaita wuta
  • Rahoto ya nuna cewa fatan miliyoyin 'yan Najeriya ya kama hanyar rushewa saboda gaza cimma matsaya a tattaunawar Islamabad
  • Amurka da Iran sun tashi baram-baram a zaman sulhun da suka yi a karshen mako, lamarin da ka iya zama barazana ga mashigar Hormuz

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Fatan da ‘yan Najeriya ke yi na ganin saukar farashin man fetur ya samu koma baya bayan rugujewar tattaunawa sulhu tsakanin Amurka da Iran.

Rashin cimma matsaya a tattaunawar Irar da Amurka da ta gudana a Pakistan, ya sake tayar da hankali a Gabas ta Tsakiya tare da girgiza kasuwar mai ta duniya.

Gagunan danyen mai.
Gangunan danyen mai da ake hada-hadarsu a kasuwannin duniya Hoto: SOPA Images
Source: Getty Images

Kasuwar mai ta shiga yanayin rashin tabbas

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad

Daily Trust ta ruwaito cewa rushewar tattaunawar, wadda ta kare ba tare da cimma matsaya ba kan shirin nukiliyar Iran, ta kara tsoro kan yiwuwar rashin zaman lafiya a mashigar ruwa ta Hormuz

Kasuwannin makamashi na duniya sun shiga yanayin rashin tabbas, inda masana ke gargadin cewa farashin mai na iya sake tashi bayan dan saukar da aka gani lokacin tsagaita wuta.

Fatan 'yan Najeriya ya fara rushewa

Sai dai wannan lamari ba zai yi wa miliyoyin 'yan Najeriya da ke fatan samun saukin farashin fetur dadi ba, musamnan idan aka ci gaba da yakin Gabas ta Tsakiya.

Kafin rugujewar tattaunawar, an fara samun dan haske cewa zaman lafiya tsakanin Washington da Tehran zai iya daidaita samar da mai tare da rage tsadar da ya yi.

A lokacin da kasashen suka cimma matsayar tsagaita wuta, farashin gangar danyen mai ya sauka daga kusan Dala 120 zuwa Dala 92, kafin ya daidaita a kusan Dala 95 a karshen mako

Sai dai wannan ci gaba na iya gushewa sakamakon sabon yakin da ka iya barkewar matukar lokacin tsagaita wuta ya kare ba tare da cimma matsaya ta karshe ba.

Kara karanta wannan

Iran ta fadi dalili 1 da ya jawo aka tashi baram baram a zaman sulhu da Amurka

Fetur.
Yadda ake zuba man fetur a ababen hawa a gidan mai a Najeriya Hoto: Light Oriye
Source: Getty Images

Abin da zai jawo tashin mai a duniya

Yanzu haka, ‘yan kasuwar mai sun fara lissafa sababbin hadurran da aka iya tasowa na kasuwanci, wanda ke sa farashin mai ya karu, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Mashigar Strait of Hormuz na da matukar muhimmanci ga jigilar mai a duniya, don haka duk wani rikici a yankin na da tasiri kai tsaye kan farashi da tsaron makamashi

Masana na ganin cewa idan rikicin ya ci gaba, ba wai farashin mai kadai ba, har ma tattalin arzikin duniya zai iya fuskantar matsin lamba mai tsanani.

TUC ta yi hasashen tsadar fetur a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa TUC ta yi gargadin cewa farashin litar fetur (PMS) na iya kai wa akalla Naira 2,000 kowace lita sakamakon matsin tattalin arziki na cikin gida da na duniya.

Kungiyar yan kwadagon ta ce yakin Iran, Isra’ila da Amurka, kafin a tsagaita wuta, ya dagula hanyoyin safarar mai, wanda ya jawo tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Shugaban TUC, Festus Osifo ya bukaci gwamnatin tarayya ta bullo da tallafi a danyen man da take samar wa matatun cikin gida don ragewa yan Najeriya radadi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262