An Kama Ɗan Shekara 15 da ake Zargi da Hannu a Kashe Janar a Harin Borno
- Sojoji sun kama matashi mai shekaru 15 da ake zargi da hannu a harin Borno a ranar Alhamis 9 ga watan Afrilu, 2026
- Ana zargin matashin da alaka da kisan janar da wasu sojoji uku yayin da aka aiko shi cikin gari sayen kayan aikin ƴan ta'adda
- Ya bayyana wa jami'an tsaro yadda suka kai harin, sannan da maboyar sauran abokansa da suka kai harin tare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad, edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Dakarun rundunar hadin gwiwa ta 'Operation Hadin Kai' a yankin Arewa maso Gabas sun kama wani matashi mai shekaru 15 da ake zargi da hannu a wani mummunan hari da ya faru a jihar Borno.
Rahotanni sun ce an kama matashin, wanda aka bayyana sunansa da Tijjani, an kama shi a ranar Lahadi 13 ga watan Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan
Dalilin gwamnan Borno na goyon bayan harin sojin sama duk da rasa rayuka akalla 200

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta wallafa cewa an kama Tijjani ne yayin da yake kan hanyarsa ta sayen abinci ga kungiyar da yake tare da su.
An kama ɗan ISWAP a jihar Borno
Business Day ta wallafa cewa majiyoyin soji sun bayyana cewa ana zargin Tijjani da alaka da harin da ya yi sanadin mutuwar wani babban jami’in soja mai mukamin birgediya janar, Oseni Braimah, tare da wasu sojoji uku.
An kashe Braimah, wanda shi ne kwamandan rundunar brigade ta 29 karkashin Operation Hadin Kai, ne a ranar Alhamis 9 ga watan Afrilu, 2927 lokacin da wasu da ‘yan Boko Haram suka kai hari kan sansanin sojoji.
A wani bidiyo da ya bayyana a yanar gizo, matashin ya ce an kama shi ne a garin Ngamdu da ke jihar Borno,ya kuma yi karin bayani kan yadda aka kama shi.
Yadda aka kama matashin ɗan ISWAP
A cewar Tijjani, ya amsa cewa ya taba shiga kai wasu hare-hare da aka kai a garuruwan Benisheik da Ngamdu.
Ya ce:
“Kafin harin, mun fito daga Jilli, sannan bayan an kai harin muka koma can. Jiya aka aiko ni daga Jilli da kudi N850,000 domin na karbo wasu kayayyakin aiki daga Ngamdu, amma sojoji suka kama ni.”

Source: Original
Matashin ya kara da cewa ya bar sauran abokan aikinsa a Jilli a ranar Asabar, 11 ga watan Afrilu, 2026 yana mai cewa bai san halin da suke ciki ba bayan barinsa wurin.
Ya ce:
“Jiya na bar sauran ‘yan kungiyar a Jilli. Ban san abin da ya faru da su a can ba.”
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da kamen matashin.
Ƴan ISWAP sun kashe jami'an soja
A baya, mun wallafa cewa ƴan ta'addan kungiyar ISWAP sun kai mummunan hari kan wani sansanin dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno a ranar Alhamis 9 ga watan Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya yi sanadiyyar mutuwar Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah, sojoji 17 da 'yan ta'adda da dama bayan an dade ana musayar wuta.
'Yan ta'addan sun kuma kashe fararen hula tare da yin satar abinci a shaguna yayin kazamin harin da suka kai wanda ya daga hankulan mazauna yankin da kewaye.
Asali: Legit.ng
