Sojojin Sama Sun Yi Kuskuren Kai Hari, Sun Kashe Fararen Hula kusan 200 a Borno

Sojojin Sama Sun Yi Kuskuren Kai Hari, Sun Kashe Fararen Hula kusan 200 a Borno

  • Jirgin yaƙin sojojin saman Najeriya ya saki wuta a kasuwar mako-mako ta Jilli da ke Yobe inda akalla mutane 200 suka riga mu gidan gaskiya
  • Jiragen yaƙin suna bin sawun ƴan ta'adda ne da suka zo karɓar haraji, sai dai an samu kuskure, inda harin ya faɗa kan talakawa ƴan kasuwa
  • Shugabannin yankin sun tabbatar da cewa an kwantar da mutane da dama a asibitin ƙwararru na Geidam, wasu kuma an tura su Damaturu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yobe – Wani mummunan hari da jirgin sojojin saman Najeriya ya kai ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula fiye da 200 a kasuwar Jilli da ke tsakanin jihar Borno da Yobe.

Harin ya faru ne a daidai lokacin da mutane ke tsaka da cinikayya a kasuwar, wadda ke tsakanin ƙananan hukumomin Gubio da Geidam.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An ji abin da ya faru Boko Haram suka kashe Janar a Borno

Sojojin saman Najeriya sun yi kuskuren kashe fiye da mutane 50 a kasuwar Yobe
Mutane sun yi dandazo a yankin kasuwar Jilli da ke Yobe inda aka ce sojojin sama sun yi kuskuren kashe 'yan kasuwa fiye da 50. Hoto: @daily_trust/X
Source: UGC

Kuskuren sojoji ya yi ajalin 'yan kasuwar Yobe

A wata sanarwa da kafar watsa labarai ta Reuters ta samu, sojojin saman Najeriya sun ce sun kashe mayakan Boko Haram masu yawa a Jalli, amma ba su ce sun farmaki kasuwar garin ba.

Yayin da jiragen yakin sojojin ke bibiyar 'yan ta'addar, an ce sun saki ruwan bama bamai kan 'yan kasuwa a yammacin ranar Asabar, inda akalla mutane 200 aka ce sun mutu.

Babban mai ba Gwamnan jihar Yobe shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Abdulsalam Dahiru (rtd), ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya bayyana cewa ƙauyen Jilli yana ƙarƙashin jihar Borno ne.

Hadimin gwamnan

"Na yi magana da shugaban ƙaramar hukumar Geidam, kuma ya sanar da ni cewa Jilli tana ƙarƙashin Gubio ne a jihar Borno," in ji shi.

An garzaya da wasu mutane asibiti

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani mazaunin yankin da ya shaida lamarin ya bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:46 na rana.

Kara karanta wannan

Mojtaba: Halin da sabon jagoran addini na Iran yake ciki kan lafiyarsa

"Na ƙirga gawarwakin mutane 56 da idona, sannan na taimaka wajen kai wasu asibiti. Ina jin adadin zai iya wuce haka domin har yanzu ana ci gaba da gano gawarwaki," in ji majiyar.

Malam Lawan Zanna, kansilan mazaɓar Fichimaram, ya tabbatar da cewa an garzaya da mutane da dama asibitin ƙwararru na Geidam.

Kansilan ya bayyana cewa lokacin da mutane suka hango isowar jiragen, sai suka fara gudun ceton rai, amma duk da haka bama-baman da aka jeho suka tashi a kansu.

Ana fargabar jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya yi luguden wuta kan fararen hula a Borno.
Jirgin yakin sojojin saman Najeriya. Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

Rundunar sojojin sama ta yi gum

Malam Lawan Zanna ya ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka kai asibiti, mutane tara sun riga sun mutu.

Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin saman Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa ba game da wannan zargi na kuskuren harin da ya rutsa da farar hula.

Wannan kasuwa dai tana tattara mutane ne daga Gubio, Geidam, da Benisheikh, wanda hakan ya sa asarar ta shafi iyalai da dama a yankunan biyu.

Sojoji sun kashe mutane a Borno

A wani labari, mun ruwaito cewa, harin jiragen sojojin sama ya hallaka fararen hula da dama a jihar Borno, sa’o’i bayan rundunar ta jaddada kare rayukan jama’a.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur: Tinubu ya nuna kukan dadi 'yan Najeriya ke yi

An rahoto cewa masunta da direbobi ne suka mutu a wannan hari, wanda aka ce sojoji sun kai bayan samun bayan sirri.

Masu sharhi sun bukaci a biya diyya ga wadanda abin ya shafa tare da kara inganta binciken ISR kafin kai hare-hare ta sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com