Magana Ta Fito: An Ji Abin da Ya Faru Boko Haram Suka Kashe Janar a Borno

Magana Ta Fito: An Ji Abin da Ya Faru Boko Haram Suka Kashe Janar a Borno

  • An sake samun bayanai game da kisan Birgediya-janar Oseni Braimah a wani harin Boko Haram da ya faru a jihar Borno
  • An ce Braimah ya mutu a harin Boko Haram a Borno yayin jagorantar mayakan sa, lamarin da ya sake jefa Najeriya cikin jimami mai tsanani
  • Hukumar soji ta musanta rahoton mutuwar sojoji 17, ta ce jami’ai biyu da sojoji biyu ne kawai suka rasa rayukansu a wannan farmaki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Najeriya ta sake shiga jimami bayan mutuwar Birgediya-Janar Oseni Omoh Braimah, wanda aka kashe a harin Boko Haram a Borno tare da wasu sojoji.

Wannan rashi ya taba zuciyar yan Najeriya da dama tare da kara tayar da maganganu game da mutuwar manyan sojoji a yaki da ta'addanci.

Kara karanta wannan

Kisan Janar: Kashim Shettima ya kai ziyara Borno, ya isar da sakon Tinubu

Sojoji sun yi magana kan Janar da aka kashe a Borno
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-janar Waidi Shaibu da dakarunsa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Rahoton Vanguard ya ce marigayin ya kasance kwamandan rundunar 29 a Benisheikh da ke jihar Borno.

Sojoji da aka hallaka a harin Borno

Mahukuntan soji sun tabbatar da cewa an samu asarar rayuka yayin artabu mai tsanani da ‘yan ta’adda da suka kai hari sansanin soji da sassafe, harin ya dauki lokaci mai tsawo.

Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya kasance mai tsari, inda aka yi musayar wuta na tsawon lokaci kafin daga karshe sojoji suka fatattaki maharan daga wurin.

Sojoji sun bayyana yadda aka kashe kwamandan, suna cewa motarsa ta MRAP mai kariya ta tsaya na dan lokaci ne yayin da yake jagorantar mayar da martani a tsakiyar fada.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Operation HADIN KAI, Sani Uba, ya ce rahoton mutuwar sojoji 17 ciki har da kwamanda ba gaskiya ba ne kuma yaudara ce.

Ya jaddada cewa rahoton hukuma daga hedkwatar tsaro ya nuna jami’ai biyu da sojoji biyu ne kawai suka mutu yayin artabun da aka yi.

Kara karanta wannan

Iran ta faɗi babban matsalar Amurka a shirin yarjejeniyar zaman lafiya

Yadda yan Boko Haram suka kashe Birgediya-janar a Borno
Taswirar jihar Borno da ke fama da hare-haren Boko Haram. Hoto: Legit.
Source: Original

Mutuwar Janar Braimah ta ta rikita mutane

Mutuwar Janar Braimah ta sake nuna irin hadarin da manyan jami’an soji ke fuskanta a wannan yaki mai tsawo da ake yi a Arewa maso Gabas.

Duk da nasarorin da aka samu kan Boko Haram da ISWAP, har yanzu suna kai hare-hare masu tsari kan kauyuka da sansanonin soji.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai hari daga bangarori da dama, lamarin da ke nuna cewa sun shirya sosai kafin kai farmakin.

An yi artabu na tsawon sa’o’i da dama kafin sojoji suka tilasta maharan ja da baya, amma an samu asarar rayuka ciki har da babban jami’i, cewar Punch.

Abokan aikinsa sun bayyana shi a matsayin jajirtaccen jami’i mai kusanci da dakarunsa, wanda ke jagorantar aiki daga gaba domin karfafa gwiwar sojoji.

Abokan karatunsa sun tuna da shi a matsayin mutum mai kwarewa, ladabi da jarumta tun daga makarantar sakandare, suna cewa yana da makoma mai girma a gaba.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Sojoji sun ba hammata iska yayin ziyarar Tinubu a Bayelsa, bidiyo ya fito

Boko Haram ta saki bidiyon mata a Borno

A wani labarin, an ji cewa kungiyar 'yan Boko Haram ta fitar da wani bidiyo da ke dauke da mutanen da suka kama bayan kai wani mummunan hari jihar Borno.

Wata mata da ta yi magana ta bayyana cewa su asalin mutanen Ngoshe ne da aka kama, inda ta bayyana halin da suke cikin dajin.

Yan Boko Haram da suka yi magana sun bayyana cewa wata kungiyar matasan jihar Borno ce ta bukaci a nuna musu halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.