Kwankwaso Ya Fara Shari’a da Hadiman Abba Kabir 4, Ya Nemi a Bi Masa Kadunsa
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shigar da ƙorafi ga DSS kan zargin cin zarafin sa ta kafafen sada zumunta
- Lamarin ya janyo gayyatar wasu hadiman gwamnatin Kano domin amsa tambayoyi kan abin da ake zarginsu
- Rikicin siyasa tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya da gwamnatin Kano na kara tsananta, inda ake zargin amfani da kafafen sada zumunta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi wa wasu hadiman Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tambayoyi kan zargin cin zarafi ta yanar gizo.
Ana tuhumar hadiman ne da bata suna, bisa ƙorafin da Rabiu Musa Kwankwaso ya shigar wanda ya ke neman a bi masa kadunsa.

Source: Twitter
Kwankwaso ya kai karar hadiman Abba Kabir
Rahotanni daga The Guardian ya bayyana cewa an gayyaci jami’an hulɗa da jama’a da wasu masu ba gwamnati shawara, ciki har da Sanusi Bature Dawakin-Tofa, Salisu Yahaya Hotoro, Ibrahim Adam da Nuhu Dambazau.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗau zafi: Kwankwaso ya sa DSS ta tsare wasu manyan hadiman gwamnan Kano
Wata majiya ta ce waɗannan hadimai sun je ofishin DSS da kansu bayan sun karɓi gayyata, inda aka tsare su na tsawon sa’o’i ana yi musu tambayoyi kan zargin da ake yi musu.
A cikin ƙorafin da aka shigar, Rabiu Kwankwaso ya zargi wasu jami’an gwamnati da shirya kamfen na bata masa suna da kuma kai masa hari ta kafafen sada zumunta musamman Facebook.
Ya ce ayyukan sun ƙaru a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya haifar da damuwa kan yadda ake amfani da yanar gizo wajen ƙara rura wutar rikicin siyasa a Kano.

Source: Facebook
Bukatar Kwankwaso ga hukumar DSS
Kwankwaso ya buƙaci DSS da ta gudanar da bincike mai zurfi tare da ɗaukar matakin da ya dace, yana mai gargadin cewa irin waɗannan ayyuka na iya kawo barazana ga zaman lafiya da siyasa.
Sai dai bayan kammala tambayoyin, an saki wasu daga cikin hadiman da beli bisa amincewar kansu, kamar yadda Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya tabbatar a Facebook.
Ya ce:
“An tsare mu na tsawon sa’o’i huɗu, daga bisani aka sake mu da beli bisa amincewar kanmu, kuma Sanata Kwankwaso zai kai lamarin kotu.”

Kara karanta wannan
APC: Tsohon saƙon shugaban INEC ya jawo zazzafar muhawara kan sahihancin zaben 2027
Masu lura da al’amuran siyasa sun ce wannan lamari na da alaƙa da rikicin da ya daɗe yana faruwa a kafafen sada zumunta tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya da gwamnatin Kano
Sun bayyana cewa ana yawan samun musayar kalamai masu zafi a tsakanin ɓangarorin biyu, inda kowanne ke zargin ɗaya da yada bayanan bata suna
Duk da haka, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Kano kan lamarin, amma mai magana da yawun gwamnan ya tabbatar da faruwar abin a shafinsa na sada zumunta.
Abba Kabir ya yi wa Kwankwaso martani
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kansa a matsayin jagoran APC a Kano bayan komawa jam'iyyar daga NNPP.
Abba Kabir ya bayyana cewa bai karkashin tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje duk da sauya sheƙarsa daga NNPP.
Gwamnan ya mayar da martani ga Rabiu Kwankwaso, inda ya ce sauya sheƙarsa ya biyo bayan rikicin cikin gida na NNPP, ya musanta zargin cin amanar Kwankwasiyya.
Asali: Legit.ng