Siyasa Ta Ɗau Zafi: Kwankwaso Ya Sa DSS Ta Tsare Wasu Manyan Hadiman Gwamnan Kano

Siyasa Ta Ɗau Zafi: Kwankwaso Ya Sa DSS Ta Tsare Wasu Manyan Hadiman Gwamnan Kano

  • Hukumar DSS ta tsare wasu hadiman Gwamna Abba Kabir Yusuf kan zargin cin zarafi a intanet da ɓata sunan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • Kwankwaso ya zargi hadiman da amfani da dandalin Facebook da kuma waƙar Dauda Kahutu Rarara wajen hantararsa, da bata masa suna
  • An saki dukkan hadiman a kan belin kansu bayan sun shafe sa’o’i huɗu ana titsiye su a ofishin hukumar tsaron ta farin kaya da ke Kano

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano – Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a jihar Kano ta gudanar da bincike mai zurfi kan wasu hadiman Gwamna Abba Kabir Yusuf guda biyar a ranar Asabar, 11 ga Afrilu, 2026.

Wannan mataki ya biyo bayan wata takarda da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya aike wa hukumar.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fara shari'a da hadiman Abba Kabir 4, ya nemi a bi masa kadunsa

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai karar wasu hadiman gwamnan Kano ga hukumar DSS.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso (hagu), Sanusi Bature Dawakin Tofa (tsakiya), da Gwamna Abba Yusuf (dama). Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

DSS ta tsare hadiman gwamnan Kano

Hadiman da aka titsiye sun haɗa da babban mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa da Salisu Yahaya Hotoro, kamar yadda rahoton The Guardian ya nuna.

Sauran wadanda DSS ta tsare sun hada da Ibrahim Adam; Nuhu Dambazau; da kuma Mukhtar S. Yahuza. Bayanan sun nuna cewa hadiman sun kai kansu ofishin DSS ne bayan samun sammaci.

A cikin takardar ƙarar mai kwanan wata 10 ga Afrilu, 2026, wadda Sanata Kwankwaso ya sanya wa hannu a ƙarƙashin inuwar tafiyar Kwankwasiyya, ya zargi hadiman gwamnatin Kano da kitsa yaƙin neman zaɓe na ɓata suna a kafofin sada zumunta, musamman Facebook.

Kwankwaso, wanda kwanan nan ya koma jam'iyyar ADC, ya bayyana cewa waɗannan hare-hare na intanet suna neman lalata martabarsa da kuma tada zaune tsaye a jihar Kano.

Takardar ta ce:

"Ya bayyana karara cewa wasu mutane da ke riƙe da muƙaman gwamnati a jihar Kano ne ke rura wutar wannan cin zarafi a yanar gizo."

Kara karanta wannan

DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya

Sakin hadiman Da Kuma Matakin Kotu

Bayan kwashe sa’o’i huɗu ana musu tambayoyi, hukumar DSS ta saki hadiman a kan belin kansu, kamar yadda Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook.

"Hukumar DSS, reshen Kano ta bada beli na da na wasu mutane uku; Salisu Yahaya Hotoro, Ibrahim Adam da Hon. Nuhu Dambazau, bayan ta samu korafi daga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan zargin laifuffukan intanet, hantara da kuma bata suna.
"Mun shafe awanni hudu a tsare a hannun DSS kafin a bada mu beli. Sanata Kwankwaso ya shirya gufanar da mu a gaban kotu kan wannan batu."

- Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi hadiman gwamnan Kano da bata masa suna.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya na jawabi a wani taro a Kano, nesa da shi daga dama, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne da jar hula. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Zargin bata sunan Kwankwaso a Waka

A wani sakon na daban da Sanusi Bature ya wallafa a shafinsa na Facebook, hadimin gwamnan ya ce daga cikin zarge-zargen da Kwankwaso yake yi, har da batun wata waka da Dauda Kahutu Rarara ya yi.

Mai magana da yawun gwamnan ya ce:

Kara karanta wannan

APC na tsakiyar zawarcin Shekarau, Tinubu zai narka kusan Naira biliyan 4 a Kano

"Daya daga cikin abun da Jagora ke tuhuma ta har da batun wakar Rarara wai shi nasa ake kira Risi."

Abba ya yi martani mai zafi ga Kwankwaso

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kansa a matsayin jagoran APC a Kano bayan komawa jam'iyyar daga NNPP.

Mai girma gwamnan Kano, Abba Kabir ya bayyana cewa bai karkashin tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje duk da sauya sheƙarsa daga NNPP.

Gwamnan ya mayar da martani ga Rabiu Kwankwaso, inda ya ce sauya sheƙarsa ya biyo bayan rikicin cikin gida na NNPP, ya musanta zargin cin amanar Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com