Kisan Janar: Kashim Shettima Ya Kai Ziyara Borno, Ya Isar da Sakon Tinubu
- 'Yan ta'addan ISWAP da Boko Haram sun hallaka sojojin Najeriya ciki har da Birgediya Janar a wani hari da suka kai a jihar Borno
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ka ziyara birnin Maiduguri domin jajantawa kan mummunan lamarin
- Kashim Shettima ya kai ziyarar ta'aziyyar ne a jihar Borno a madadin shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ziyarci Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin jajantawa rundunar sojojin Najeriya da gwamnatin jihar.
Kashim Shettima ya je jaje ne kan harin da aka kai wa jami’an sojoji kwanan nan a Benisheikh, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’ai da sojoji da dama, ciki har da Birgediya Janar Oseni Braimah.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Kashim Shettima, Stanley Nkwocha, ya fitar a shafinsa na X aranar Asabar, 11 ga watab Afrilun 2026.
Shettima ya je ta'aziyya a madadin Tinubu
Stanley Nkwocha ya bayyana cewa Shettima ya kai ziyarar ne a madadin Shugaba Bola Tinubu.
Shettima ya bayyana cewa jaruman sojojin sun rasu ne yayin gudanar da hidima ga ƙasa, inda ya bayyana sadaukarwar tasu a matsayin wadda ke nuna muhimmancin zaman lafiya da tsaro.
“Waɗannan mutanen sun saka kaya ne saboda dukkanmu. Sun tsaya ne domin kare al’ummominmu, iyalanmu, da makomar yaranmu. Jarumtakarsu tana tunatar da mu cewa zaman lafiya da tsaro sukan zo ne da babban haraji mai tsada."
- Kashim Shettima
Gwamnatin Tinubu na farautar 'yan ta'adda
Ya ba da tabbacin ci gaba da samun goyon bayan gwamnatin tarayya, inda ya ce, “masu aikata laifuffuka ba za su sami wurin ɓuya ba a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
Wannan ziyarar ta’aziyya na zuwa ne bayan wani mummunan hari na tsakar dare da aka kai wa sansanin soji a Benisheikh, jihar Borno.

Kara karanta wannan
Sunayen manyan jami'an sojin Najeriya da suka mutu a bakin aiki daga 2016 zuwa 2026

Source: Twitter
'Yan ta'adda sun yi barna a Borno
Ana zargin mayakan Boko Haram da na ISWAP sun ƙaddamar da hare-hare a lokaci guda kan wuraren sojoji da dama da misalin ƙarfe 12:30 na dare a ranar Alhamis.
An ce maharan sun zo ne da yawa, inda suka farmaki aƙalla sansanonin sojoji guda uku kafin su wuce zuwa yankunan fararen hula da ke maƙwabtaka.
Jaridar The Punch ta ce wani soja da ya tsira daga harin ya bayyana cewa girman harin da yadda aka tsara shi, inda ya lura cewa maharan kamar sun riga sun yi nazarin wuraren da sojojin suke kafin su kawo harin.
Dan El-Rufai ya ba Shettima hakuri
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Bashir El-Rufaii, ya nemi afuwa ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Afuwar da dan tsohon gwamnan na Kaduna ya nema ta biyo bayan wallafa wani sako da ya yi da ya ke sukar Kashim Shettima a matsayin marar tasiri.
Bashir ya bayyana cewa kalamansa na baya sun kasance kuskure kuma marasa dacewa, yana mai cewa yana girmama Shettima sosai.
Asali: Legit.ng
