Kano Ta Yi Babban Rashi: Kanin Sarki Sanusi II Ya Yi Bankwana da Duniya
- Masarautar Kano da jihar ta yi babban rashin bayan sanar da rasuwar kanin Sarki Muhammadu Sanusi II wanda ya rikita yan uwansa
- An tabbatar da rasuwar Salihi Aminu Sanusi kanin Sarkin Kano lamarin da ya jefa iyalai, abokai da masoya cikin jimami mai tsanani
- Masu alhini sun yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya jiƙansa da rahama, tare da roƙon Ubangiji ya ba iyalansa haƙuri
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An shiga cikin alhini a Kano bayan masarautar jihar ta yi rashin daya daga cikin 'ya'yanta wanda ya tayar da hankulan yan uwa da abokan arziki.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi babban rashin Salihi Aminu Sanusi, ƙanin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Source: Twitter
Masarautar Kano ta yi babban rashi
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin Masarautar wanda ya wallafa a X a yau Asabar 11 ga watan Afrilun 2026 da muke ciki
Wannan lamari ya haifar da jimami a tsakanin dangi, abokai da masu kaunarsa wadanda suka yi masa addu'ar fatan alheri da samun rahama a gobe kiyama.
An bayyana cewa an yi jana’izar marigayin a ranar Asabar 11 ga watan Afrilun 2026 da misalin ƙarfe 11:00 na safe a Kofar Kudu da ke cikin Fadar Sarkin Kano, inda ake sa ran jama’a da dama za su halarta domin yi masa bankwana.

Source: Twitter
Yadda mutane suka shiga jimami saboda rashin
Mutane da dama sun nuna alhini tare da yin addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa kura-kuransa, ya jiƙansa da rahama, ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdausi.
Haka kuma, an roƙi Allah ya ba iyalansa, abokansa da dukkan masoyansa haƙuri da juriya domin jure wannan babban rashi da suka yi wanda zai yi wahalar cike gurbinsa.
Sanarwar ta ce:
"Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un !
"Salihi Aminu Sanusi, ƙanin Mai Martaba Sarkin Kano, ya rasu. Za a gudanar da jana’izarsa gobe Asabar da ƙarfe 11:00 na safe a Kofar Kudu, Fadar Sarkin Kano.

Kara karanta wannan
Tirkashi: Sojoji sun ba hammata iska yayin ziyarar Tinubu a Bayelsa, bidiyo ya fito
"Allah Ya jiƙansa da rahama. Amin."
Mutane da dama sun yi tsokaci kan sanarar da aka fitar game da babban rashi da Sarki Sanusi II da masarautar Kano ta yi.
Mafi yawan wadanda suka tofa tofa albarkacin bakinsu sun yi ta yi wa marigayin addu'o'in samun rahama a gobe kiyama.
Kano: Sarkin Gabas ya riga mu gidan gaskia
A baya, mun ba ku labarin cewa Masarautar Kano ta tabbatar da rasuwar Sarkin Gabas, Hakimin Kabo, Alhaji Idris Muhammad Adamu DanKabo, bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi.
Bayanai daga shafin Sanusi II Dynasty sun bayyana cewa marigayin ya kasance shugaba mai saukin kai, mai kyakkyawar mu’amala da jama’a.
Masarautar ta yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya jikansa da rahama, ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdausi mai daraja tare da ba iyalansa hakurin jure wannan rashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
