Najeriya Ta Yi Rashin Ɗan Majalisa daga Kano, Hon Danjuma Ya Rasu
- Majalisar wakilan Najeriya ta yi jimamin rasuwar dan majalisa daga Kano, Hon Muhammad Danjuma Hassan
- Hon Muhammad Danjuma Hassan ya rasu yana da shekaru 66 a Abuja bayan jinya da ya sha fama da ita
- Kafin rasuwarsa, shi ne ɗan majalisar mai wakiltar mazabar Dawakin Kudu/Warawa a jihar Kano da ake yi wa gogaggen ɗan siyasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Majalisar wakilai ta kasa ta sanar da rasuwar daya daga cikin mambobinta, Hon. Muhammad Danjuma Hassan, wanda ke wakiltar mazabar Dawakin Kudu/Warawa a jihar Kano.
Majalisa ta bayyana cewamarigayin ya rasu ne a yammacin ranar Juma’a, 10 ga watan Afrilu, 2026, a birnin Abuja, bayan fama da jinya.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ofishin kakakin majalisar ya fitar kuma aka wallafa a shafin Facebook na majalisa, an bayyana cewa ya rasu yana da shekaru 66.
Ɗan majalisar Kano ya rasu
Hon. Muhammad Danjuma Hassan, ya samu shiga majalisar wakilai ne a shekarar 2023 karkashin jam’iyyar NNPP.
Kafin shiga siyasa, ya yi aiki a majalisar dokoki ta kasa, inda ya taso daga matakai daban-daban har zuwa mukamin babban sakatare.
Sanarwar ta bayyana cewa rasuwarsa babban rashi ne ba kawai ga majalisar wakilai ba, har ma da al’ummar mazabarsa da daukacin kasar nan.
An bayyana shi a matsayin daya daga cikin fitattun kwararrun masu tsara dokoki a Najeriya, wanda gudunmawarsa ta taka rawa wajen bunkasa dokoki da tsarin mulki a tsawon shekaru.

Source: UGC
Majalisar ta jaddada cewa yawancin dokokin da aka samar a shekarun baya sun samu tasiri daga irin kwarewa da iliminsa a fannin shari’a da tsara dokoki.
A majalisar wakilai, marigayin ya rike mukamin mataimakin shugaban kwamitin shari’a, inda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen karfafa tsarin shari’a da tabbatar da bin doka a kasa.
Ana jimamin rasuwar ɗan majalisar Kano

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya
Baya ga haka, ya kasance mamba a kwamitoci da dama da suka hada da na korafe-korafen jama’a, sufurin jiragen sama, ma’adanai, gyaran kundin tsarin mulki, da kuma yarjejeniyoyi da hulda da kasashen waje.
A dukkannin ayyukansa, an san shi da kwarewa, nutsuwa, da kuma jajircewa wajen hidimar jama’a, a cewar sanarwar.
Haka kuma, an yaba masa da tawali’u da kokarinsa na samar da fahimtar juna da hadin kai a tsakanin ‘yan majalisa.
Shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, al’ummar mazabarsa, gwamnatin jihar Kano da daukacin ‘yan Najeriya.
An sanar da cewa za a yi jana’izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci a ranar Asabar, 11 ga Afrilu, 2026, yayin da za a sanar da karin bayani daga baya.
Majalisar ta roki Allah da Ya jikansa, Ya kuma ba iyalansa da daukacin al’umma hakurin jure wannan babban rashi.
Ɗan majalisar Kebbi ya rasu
A baya, mun wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa an tabbatar da rasuwar shugaban majalisar dokokin Jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru a kasar waje.
Shugaban ya rasu ne a wani asibiti a kasar Masar bayan jinya kan wata cuta da ba a bayyana ga manema labarai ba har zuwa lokacin da aka yi masa sutura ba.
Gwamnatin jihar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Kebbi da kasa baki daya yayin da ta yi masa addu'a Allah SWT ya yi masa rahama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
