Tirkashi: Sojoji Sun ba Hammata Iska yayin Ziyarar Tinubu a Bayelsa, Bidiyo Ya Fito
- Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kai ziyarar aiki zuwa jihar Bayelsa domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnati ta gudanar
- Ziyarar shugaban kasar ta bar baya da kura bayan da wasu dakarun sojoji da ke cikin masu yi masa rakiya a tafiyar suka gwabza fada a tsakaninsu
- Sojojin dai sun gwabza fada ne a kan titi yayin da jama'a suka tsaya suna kallon abin da ke faruwa cike da mamaki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bayelsa - Jami'an sojojin Najeriya sun ba hammata iska a jihar Bayelsa da ke yankin Kudu maso Kudu.
An hango jami’an sojojin Najeriya suna dambe da juna a jihar Bayelsa yayin ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Juma’a, 10 ga watan Afrilun 2026.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoton fadan da aka yi tsakanin jami'an sojojin a jihar Bayelsa.
Sojoji sun ba hammata iska
A cikin wani faifan bidiyo mai tsawon daƙiƙa 53 da ke yawo a yanar gizo, an ga matuƙin wata motar Hilux da aka rubuta “Naval Police” a jikinta ya fito daga motarsa yana musayar kalamai da wani matuƙin wata motar.
Shafin Bayelsan Pride a manhajar X ya sanya bidiyon artabun da sojojin suka yi yayin ziyarar ta Shugaba Bola Tinubu.
Jim kaɗan bayan ya koma cikin motarsa, sai wani soja ɗauke da bindiga ya nufo shi, inda ya kai wa matuƙin motar ta 'Naval Police' naushi, lamarin da ya janyo rikici.
Nan take lamarin ya rikide zuwa fada, inda jami’an da ke tattare da motocin biyu suka rinka dukan juna, yayin da fararen hula suka tsaya cike da mamaki suna kallo.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a kai ga gano musabbabin takun-saƙar ba wanda ya auku tsakanin jami'an sojojin kasa da sojojin ruwa.

Kara karanta wannan
Sunayen manyan jami'an sojin Najeriya da suka mutu a bakin aiki daga 2016 zuwa 2026
Shugaba Tinubu ya ziyarci Bayelsa
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya faru ne a daidai lokacin da Shugaban ƙasar ke barin wurin wani taro yayin ziyararsa a jihar Bayelsa.

Source: Facebook
Shugaba Tinubu ya ziyarci Bayelsa ne domin ƙaddamar da wasu ayyuka, inda a wurin ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar.
Ya yi alƙawarin ci gaba da zuba jari ga dakarun tsaron ƙasar, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba wa jami’an tsaro kayan aiki da horon da ya dace domin tunkarar ta’addanci, fashi da makami, da sauran barazanar tsaro.
Kalli bidiyon a nan:
An kashe sojoji a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta tabbatar da kashe wasu dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare a ranar 9 ga Afrilu, 2026, lokacin da maharan suka yi ƙoƙarin kutsa kai cikin katangar tsaro ta sansanin sojojin.
Hedikwatar Tsaron ta bayyana harin a matsayin alamar fitar da rai daga ɓangaren ’yan ta'adda, wadanda ke fuskantar koma baya a hannun dakarun sojoji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
