Bayan Tsagaita Wuta a Yakin Iran, An Ji Abin da Zai Sa Litar Fetur Ta Haura N2,000 a Najeriya
- Kungiyar TUC ta bayyana cewa matsin tattalin arziki da ake fuskanta sakamakon yakin Iran da Amurka zai kara tashin farashin fetur a Najeriya
- Duk da an tsagaita wuta a yan kwanakin nan, TUC ta ce farashin litar fetur na iya haura N2,000, wanda hakan zai jefa mutane cikin kunci
- Shugaban TUC, Festus Osifo ya bukaci gwamnatin tarayya ta bullo da tallafi a danyen man da take samar wa matatun cikin gida
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kungiyar 'Yan Kwadago ta TUC ta yi gargadin cewa farashin man fetur (PMS) na iya kai wa akalla Naira 2,000 kowace lita sakamakon matsin tattalin arziki na cikin gida da na duniya.
Shugaban kungiyar TUC na kasa, Festus Osifo, ya bayyana haka a Abuja ranar Alhamis, 10 ga watan Afrilu, 2027.

Kara karanta wannan
2027: Majalisar Shari'ar musulunci da kungiyoyi 3 da suka nemi a canza shugaban INEC

Source: UGC
Abin da zai kara tashin fetur a Najeriya
Ya danganta yiwuwar karin farashin da rikicin Amurka/Isra'ila da kasar Musulunci ta Iran ke haifarwa, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.
Ya ce yakin Iran, Isra’ila da Amurka, kafin a tsagaita wuta, ya dagula hanyoyin safarar mai, wanda ya jawo tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Osifo ya ce karin farashin fetur na iya sake jefa ‘yan Najeriya cikin wahala da kuncin rayuwa, inda a wasu yankuna kowace litar fetur ta kusa kai wa N2,000.
“Ma’aikatan Najeriya na cikin matsananciyar wahala a yanzu,” in ji shi, yana mai cewa tasirin hakan ya shafi sufuri, masana’antu da kuma tsadar rayuwa gaba daya.
TUC ta hango karin tsadar rayuwa
Ya kara da cewa tashin farashin dizal ya kara kudin samar da kayayyaki, wanda hakan ke komawa kan talakawa ta hanyar karin farashin kaya da ayyuka.
Domin magance matsalar, Osifo ya bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da tallafi ga danyen mai da ake ba matatun cikin gida, musamman idan farashin ya wuce wanda aka tsara a kasafin kudi.

Kara karanta wannan
Amurka da Iran na tsagaita wuta, matatar Dangote ta sauya farashin fetur a Najeriya
A cewarsa, hakan zai rage kudin tace mai tare da saukar da farashin fetur, dizal da man jirgin sama cikin kankanin lokaci.
Osifo ya kuma nuna cewa faduwar darajar Naira na daga cikin manyan abubuwan da ke kara tsadar mai, yana mai cewa daidaiton canjin kudi na da muhimmanci wajen rage hauhawar farashi.

Source: Getty Images
Mene ne mafiya daga wannan matsala?
A matsayin mafita ta dogon lokaci, ya bukaci a kara zuba jari a bangaren samar da ababen amfani da iskar gas mai (CNG) a fadin kasar, cewar rahoton Leadership.
Ya ce amfani da motocin CNG zai rage dogaro da fetur, amma yai cewa rashin wadatattun wuraren sanya gas na daga cikin manyan kalubale, inda ya ba shawarar samar da gidajen zuba gas a manyan tituna.
Dangote ya janye karin kudin fetur
A wani labarin, kun ji cewa a kokarin samar da sauki ga yan Najeriya, matatar man Dangote ta sanar da janye ƙarin farashin man fetur da ta yi a baya bayan nan.
Da farko dai an samu labarin cewa matatar man Dangote ta sauya farashin litar fetur zuwa ₦1,275 daga ₦1,200 a daren ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026.
Sai dai jim kadan bayan haka, matatar ta janye wannan kari da ta yi, inda ta maida farashin kowace litar zuwa zuwa ₦1,200 sakamakon gagarumar faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Asali: Legit.ng