An Yanke wa Ɗan Takarar Sanata Hukuncin Ɗaurin Shekaru 10 kan Alaka da Boko Haram
- Kotu ta yanke wa Babagana Habeeb hukuncin shekaru 10 a gidan yari saboda taimaka wa ƴan ta'adda ta hanyar sayar masu da man fetur
- A zaman kotun, lauyan gwamnati ya bayyana cewa Boko Haram ta yi amfani da fetur din da Babagana ya sayar masu wajen kai hare hare
- Amma abin mamaki, kotu ta bada umarnin a saki Babagana bayan yanke masa hukunci, duk da cewa gwamnati ta nemi a daure shi shekaru 20
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wani tsohon ɗan takarar Sanata daga Jihar Borno, Babagana Habeeb, hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari.
An same shi da laifin sayar wa ƴan ta'addan Boko Haram man fetur, wanda hakan ya saba wa dokokin yaƙi da ta'addanci na Najeriya.

Kara karanta wannan
'Za mu ci gaba da kai hari,' Isra'ila ta sake tsokano Iran da ta kashe mutane a Lebanon

Source: UGC
An yanke wa tsohon dan takara hukuncin dauri
An yanke wa Habeeb, wanda ya tsaya takarar sanata a zaɓen 2015 hukunci ne a kan tuhuma guda ɗaya ta taimaka wa ta'addanci, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Mai shari'a Peter Lifu ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta samu nasarar tabbatar da laifin da ake zargin tsohon dan takarar majalisar dattawan ya aikata, don haka aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 10.
Wanda aka yanke wa hukuncin, wanda ɗan kasuwar mai ne a Maiduguri, ya amince a gaban kotu cewa ƴan tada ƙayar baya sun sayi fetur a gidan man sa.
Sai dai ya yi iƙirarin cewa ma'aikatansa ne suka gudanar da cinikin, ba shi da kansa ba.
Zargin sayar wa Boko Haram fetur
A lokacin da ake gudanar da shari'ar, Habeeb ya rika tsugunawa a kan gwiwowinsa a gaban alkali yana neman afuwa, inda ya bayyana cewa yana da mata biyu da ƴaƴa shida waɗanda suka dogara da shi yau.
Babagana Habeb ya kuma shaida wa kotu cewa ya shafe shekaru 10 a tsare ba tare da ganin iyalinsa ba, in ji rahoton Channels TV.
Sai dai lauyan gwamnati, Mr. David Kaswe, ya yi adawa da neman sassaucin, yana mai cewa man fetur ɗin da Habeeb ya samar ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Kaswe ya jaddada cewa ƴan ta'adda ba za su iya yin amfani da babura wajen kai hare-hare ko tserewa zuwa cikin daji ba muddin ba su da man fetur.

Source: Original
Hukuncin kotu da sakin Habeeb
Yayin yanke hukunci, Mai shari'a Lifu ya lura cewa babu wata shaida da ke nuna Habeeb mamba ne na Boko Haram ko kuma ya samu horon makami yau. Alkali ya ce babban laifinsa shi ne sayar wa ƴan ta'addan mai.
Ganin cewa Habeeb ya shafe shekaru 10 a tsare kafin a kai ga yanke hukunci, alkali ya ce wannan lokacin ya dace da hukuncin da aka ba shi.
Don haka, kotun ta ba da umarnin sakin Babagana Habeeb nan take da zarar an sanya hannu a takardar sakin sa, tare da bada shawarar cewa a sanya shi a shirin gyara hali kafin ya shiga jama'a.
Boko Haram ta saki bidiyon mutanen da ta kama
A wani labari, mun ruwaito cewa, Boko Haram ta fitar da wani bidiyo da ke nuna halin da mutane 416 da aka sace a Ngoshe, ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno suke ciki.
'Yan ta'addan sun tabbatar da cewa mutanen da suka kama, wanda galibinsu mata ne suna cikin koshin lafiya kuma ba a azabtar da su ko cin zarafinsu ba.
Kungiyar ta bayyana cewa sun saki bidiyon ne bisa buƙatar wata ƙungiya, wadda ya tabbatar tana taka rawa a matsayin mai shiga tsakani tun lokacin da aka kama mutanen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

