Sanata a Najeriya Ya Rasu, Wike Ya Fashe da Kuka yayin Jana’izar Marigayin

Sanata a Najeriya Ya Rasu, Wike Ya Fashe da Kuka yayin Jana’izar Marigayin

  • An gudanar da jana'izar wani sanata a Najeriya a birnin Port Harcourt wanda ya samu halartar manyan mutane a kasar
  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kasa rike hawaye yayin jana’izar marigayi Sanata Barinada Barry Mpigi a Port Harcourt
  • Marigayi Sanata Mpigi, wanda ya wakilci mazabar Rivers ta Kudu maso Gabas karkashin PDP ya rasu yana da shekaru 64

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya fashe da kuka yayin jana'izar marigayi Sanata Barinada Barry Mpigi.

Ministan ya gagara rike hawaye yayin da yake yi wa marigayi Sanata Mpigi bankwana a birnin Port Harcourt da ke Rivers.

Wike ya yi kuka a jana'izar sanatan Najeriya
Ministan Abuja, Nyesom Wike yayin wani taro a Abuja. Hoto: @GovWike.
Source: Twitter

Nyesom Wike ya yi kuka wurin jana'izar sanata

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Legit Hausa ta samu wanda shafin @PH_Socials ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Sanata ya bayyana mutanen da suka haddasa rikicin PDP

Wike, wanda tsohon gwamnan Rivers ne sau biyu, ya tuna yadda marigayin ke ziyartar gidansa a Abuja tare da tabbatar masa da biyayya a kowane lokaci.

Ya ce marigayin kan ce masa, “Baba, ba zan taba barinka ba,” yana mai nuna irin kusancin da ke tsakaninsu kafin rasuwarsa.

Takaitaccen tarihin marigayi Sanata Barinada Barry Mpigi

Sanata Mpigi, wanda ya wakilci mazabar Rivers Kudu maso Gabas, ya rasu yana da shekaru 64 a ranar 19 ga Fabrairun 2026.

An haife shi a ranar 23 ga Yuni, 1961, kuma ya kasance sanata mai ci a lokacin da rasuwa ta riske shi.

Marigayin ya fara zama dan majalisar wakilai a shekarun 2011 da 2015 kafin daga bisani ya zama sanata a 2019 karkashin jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

An sake zabensa a 2023, inda ya ci gaba da wakiltar mazabarsa har zuwa rasuwarsa wanda ya tayar da hankulan yan mazabarsa.

An yi jana'izar sanatan Najeriya da ya mutu
Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike na jawabi ga manema labarai a Abuja. Hoto: @GovWike.
Source: Twitter

Wasu sanatocin da suka mutu a majalisar nan

A majalisa ta tara, ya rike mukamin shugaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa kan binciken satar danyen mai a yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan

Za a jika wa APC aiki, tsohon jagoran yakin neman zaben Tinubu a Zamfara ya koma ADC

Mpigi shi ne sanata na hudu da ya rasu tun bayan kafuwar majalisa ta 10 bayan zaben shekarar 2023 da ya gabata.

Sauran sanatocin da suka rasu sun hada da Ifeanyi Ubah, Okey Ezea da Godiya Akwashiki wanda ya rasu a kasar Indiya.

Bayanin da Wike ya yi a wajen jana’izar ya jawo martani daga ‘yan Najeriya a kafafen sada zumunta.

Wasu sun bayyana mutuwar a matsayin tunatarwa kan cewa rayuwa ba ta dawwama, yayin da wasu ke ganin ‘yan siyasa ba sa daukar darasi daga irin wadannan abubuwa.

An yi jana'izar Sanata Godiya Akwashiki

Mun ba ku labarin cewa an yi jana'iza da kuma birne marigayi sanatan Nasarawa ta Arewa, Godiya Akwashiki a gidansa da ke birnin Lafiya.

Sanata Godiya Akwashiki ya rasu ne bayan fama da jinya a wani asibiti a kasar Indiya, yana da shekaru 52 da haihuwa a duniya.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda ya halarci jana'izar, ya ce rasuwar Sanatan babban rashi ne ga Najeriya baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.