Boko Haram Ta Saki Bidiyon Mutanen da Ta Kama, Mata Sun Roki Tinubu, Shettima
- Kungiyar 'yan Boko Haram ta fitar da wani bidiyo da ke dauke da mutanen da suka kama bayan kai wani mummunan hari jihar Borno
- Wata mata da ta yi magana ta bayyana cewa su asalin mutanen Ngoshe ne da aka kama, inda ta bayyana halin da suke cikin dajin
- 'Yan Boko Haram da suka yi magana sun bayyana cewa wata kungiyar matasan jihar Borno ce ta bukaci a nuna musu halin da suke ciki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Tsagin ƙungiyar Boko Haram ya fitar da wani bidiyo da ke nuna halin da mutane 416 da aka sace a Ngoshe, ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno suke ciki.
'Yan ta'addan sun tabbatar da cewa mutanen da suka kama, wanda galibinsu mata ne suna cikin koshin lafiya kuma ba a azabtar da su ko cin zarafinsu ba.

Source: Facebook
A cikin bidiyon da tashar Dandal Kura ta wallafa a Facebook, ƙungiyar ta nuna waɗanda aka sace tare da yi musu tambayoyi kan halin da suke ciki.
Dalilin sakin bidiyon Boko Haram
Wani mamba na ƙungiyar da ya yi magana a madadinsu ya ce an yi bidiyon ne bisa buƙatar wata ƙungiya mai suna Borno South Youth Alliance, wadda ya tabbatar tana taka rawa a matsayin mai shiga tsakani tun lokacin da aka kama mutanen.
Punch ta wallafa cewa mai magana da yawun, wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce:
“Mu ne Jama’atu Ahlis-Sunna Lidda’Awati Wal-Jihad ƙarƙashin jagorancin Imam Abu Umaimatul Muhajjir. Mun zo nan ne domin fayyace wasu batutuwa kamar yadda ƙungiyar Borno South Youth Alliance ta buƙata.
"Kamar yadda ku ke gani, suna cikin ƙoshin lafiya, ba mu cutar da su.
Ya ci gaba da cewa:
“Ba tare da ɓata lokaci ba, yanzu za mu juya kyamara zuwa gare su domin su yi magana kamar yadda aka buƙata kuma shugabanninmu suka umarce mu da yin wannan bidiyo.”
Bayanin wata dake hannun Boko Haram
Bayan ya juya kyamara zuwa ga wata mata daga cikin waɗanda aka sace, ya nemi ta yi magana kan halin da suke ciki tare da roƙon gwamnati.
Ta amsa da cewa:
“Mu ne mutanen Ngoshe da aka sace a lokacin harin baya-bayan nan. Mun gode wa Allah, muna cikin ƙoshin lafiya.
"Ana kula da marasa lafiya daga cikinmu, ana ba su magani. An kawo wasu daga cikin yaranmu nan ba tare da tufafi ba, amma an ba su tufafi. Muna godiya ga Allah. Sun ba mu wajen kwana kuma suna ba mu abinci.”
Ta kara da cewa:
“Muna kira ga dukkan shugabannin Najeriya, daga Shugaba Bola Tinubu, zuwa Kashim Shettima, Babagana Zulum, da Sanata Ali Ndume, Shugaban ƙaramar hukumar Gwoza.
"Dan majalisar wakilai Babawo da sauran shugabannin Gwoza. Muna roƙon ku da ku kawo mana dauki. Muna son komawa gidajenmu domin ba mu saba zama a waje ba.

Source: Original
An karyata kai hari Abuja
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta karyata wani labari da ke cewa 'yan ta'adda sun kai mummunan hari Abuja.
Wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa 'yan ta'adda sun yi kokarin kwace ikon birnin Abuja bayan gargadin Amurka.
Sai dai bayanin 'yan sanda da shaidun gani da ido a Abuja sun tabbatar da cewa babu wani hari da aka kai wajen da aka ambata a bidiyon.
Asali: Legit.ng


