Amurka Ta Sake Daukar Mataki Mai Tsauri kan Najeriya bayan Cire Jami'anta daga Abuja
- Amurka ta soke duka bukatun da 'yan Najeriya suka shigar domin neman bizar zuwa kasar a babban birnin tarayya Abuja
- Wannan mataki na zuwa ne awanni bayan Amurka ta umarci duka jami'anta da ayyukansu ba su zama wajibi ba su shirya barin Najeriya
- Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya gargadi Amurkawa da su gujewa zuwa jihohi 23 da aka sanya a rukunin gargadi na hudu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya sanar da soke dukkan bukatun neman biza da 'yan Najeriya suka shigar a lokuta daban-daban.
Bisa haka ne ofishin jakadancin ya umarci wadanda suka shigar da bukatar neman izinin tafiya Amurka da su duba imel dinsu domin sanin sababbin ranakun da aka tsara musu.

Source: Twitter
Amurka ta bukatar neman biza a Abuja
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilun, 2026.
Ofishin jakadancin ya ce ana ci gaba da gudanar da harkokin biza a Ofishin Jakadancin Amurka da ke Lagos.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa duk da wannan mataki, jami'ai za su ci gaba da ba da sauraro da kulawa da bukacin ‘yan Amurka mazauna Najeriya ne kadai muzamman masu bukatar gaggawa.
Amurka za ta kwashe jami'anta daga Abuja
Wannan ci gaban na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta umarci ma’aikatanta da aikinsu bai zama wajibi ba su bar Abuja tare da iyalansu, saboda tabarbarewar tsaro a fadin Najeriya.
A cikin sabon gargadin tafiye-tafiye, Amurka ta shawarci ‘yan ƙasar da su sake tunanin zuwa Najeriya saboda matsalolin tsaro, ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma rikice-rikicen cikin gida.
Amurka ta kuma lissafa wasu jihohi 23 daga Kudu da Arewacin Najeriyar, inda ta ce suna da haɗari kuma ta shawarci Amurkawa da kada su kuskure su je wadannan jihohi.
Amurka ta hana yan kasar zuwa jihohi 23
Bugu da kari, ta gargaɗi ƴan ƙasarta da su guji tafiya zuwa waɗannan jihohi guda 23 da ta ɗora su a mataki na huɗu na gargaɗi saboda tabarbarewar tsaro.
“Ku sake tunani kafin tafiya zuwa Najeriya saboda laifi, ta’addanci, rikice-rikice, sace mutane da kuma rashin tabbas na samun ingantaccen kiwon lafiya. Wasu yankuna na da karin hadari,” in ji sanarwar.
Awanni kadan bayan wannan gargadi, ofishin jakadancin Amurka ya sanar da soke duk wasu bukatun neman biza, tare da maida ayyukansa zuwa jihar Legas, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Source: Twitter
Kasashe 10 sun amince da jakadun Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Amurka da wasu kasashe tara sun amince da sababbin jakadun Najeriya da aka tura masu a baya-bayan nan.
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta sanar da cewa ta karɓi takardu daga ƙasashe guda 10 da suka amince da naɗin sababbin jakadun da Shugaba Bola Tinubu ya tura masu.
Daga cikin jakadun da aka amince da su har da tsohon shugaban INEC Mahmud Yakubu da kuma tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro.
Asali: Legit.ng

