CBN Ya Fitar da Takardar N5,000 Ɗauke da Hoton Tinubu? An Gano Gaskiyar Lamarin

CBN Ya Fitar da Takardar N5,000 Ɗauke da Hoton Tinubu? An Gano Gaskiyar Lamarin

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi karin haske kan yada rahoton kirkirar takardar N5,000 a kasar
  • An yi ta yada hoton takardar N5,000 mai ɗauke da fuskar Shugaba Bola Tinubu wanda ya rikita mutane
  • Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yaɗa cewa CBN ya fitar da samfurin sabuwar takardar, amma bankin ya ƙaryata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da sanarwa game da sabuwar takardar N5,000 da ake yadawa a kasar.

Bankin CBN ya musanta rahotannin da ke yawo kan wata sabuwar takardar N5,000 mai ɗauke da hoton Shugaba Bola Tinubu.

CBN ya karyata buga sabon shugaban N5,000 da hoton Tinubu
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Yemi Cardoso a Abuja. Hoto: Central Bank of Nigeria.
Source: Twitter

CBN ya karyata fitar sabuwar takardar N5,000

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, wanda aka fi sani da Twitter a baya, CBN ya karyata labarin gaba daya.

Kara karanta wannan

Najeriya na dab da rugujewa? Minista ya faɗi gaskiyar halin da ƙasa ke ciki

Ya ce:

“Wannan bayani ƙarya ne. A kiyaye”

Bankin ya bayyana cewa wannan labari ƙarya ne kuma bai da tushe inda ya shawarci al'umma da su yi taka tsantsan kan yada rahoton.

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi iƙirarin cewa CBN ya fitar da samfurin sabuwar takardar kudin, lamarin da ya jawo muhawara mai zafi a tsakanin jama’a.

Binciken da aka gudanar kan hoton ya nuna cewa sama da kashi 90 na abin da ke ciki na fasahar AI ne, wanda ke nuna cewa an kirkire shi ne ta hanyar na’ura.

Yadda CBN ya shirya kawo N5,000 a baya

A baya, a shekarar 2012, CBN ya bayyana shirin ƙaddamar da takardar N5,000, amma daga baya a shekarar 2022 ya janye wannan shiri gaba ɗaya.

Duk da haka, doka ta bai wa bankin cikakken iko kan buga kudi, fitar da su da kuma sake rarraba su ba tare da tsoma bakin majalisa ba a duk lokacin da ya ga dama.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar APC, an kafa kwamiti game da sauya shekar gwamnan Bauchi

CBN ya ja hankalin yan Najeriya kan takardar N5,000 da hoton Tinubu
Takardar N5,000 da ake yadawa da Gwamnan CBN, Yemi Cardoso. Hoto: @cenbank.
Source: Twitter

Martanin yan Najeriya kan sanarwar CBN

Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakinsu game da sanarwar da CBN ya fitar na karyata rahoton da yan kasar ke yadawa.

12NA ya ce:

"Ba karya ba ne, kawai dai asirinku ya tonu, Tinubu ya mayar da komai na shi a Najeriya, hatta sojoji ma wakar goyon bayansa suke yi."

Qing_zaddy:

"Sai dai abin takaici mu kuma har mun fara yarda, gwamnatin tarayya sun saba karyata zarge-zarge, sai daga baya a gane zarge-zargen ashe gaskiya ne, don haka, yan Najeriya ba za su yarda da wannan shirmen kudin ba."

CBN ya kawo hanyoyin kare kudi a bankuna

A baya, mun ba ku labarin cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ta gargadi 'yan Najeriya kan yadda za su kare kudaden da suka ajiye a asusun bankunansu.

Bankin CBN ya bayyana hadarin bai wa wani lambobin sirri na PIN da na manhajar banki yayin da aikata laifuffukan damfara ke karuwa a Najeriya.

CBN ya jero muhimmam abubuwan da ya kamata masu amfani da bankuna su kiyaye don tabbatar da tsaron kudaden ajiyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.