Rundunar Sojoji Ta Tabbatar da Kashe Jami'anta, an Abin da Ta Ce kan Kisan Janar

Rundunar Sojoji Ta Tabbatar da Kashe Jami'anta, an Abin da Ta Ce kan Kisan Janar

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci kan wani sansanin sojojin Najeriya da ke a jihar Borno
  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun kashe dakarun sojoji ciki har da wani Birgediya Janar yayin harin da suka kai
  • Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta tabbatar da harin tare da kisan da aka yi wa sojojin, inda ta ce sun fatattaki 'yan ta'adda

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Hedkwatar tsaro ta tabbatar da cewa an kashe jami’an sojoji lokacin da ’yan ta'adda suka ƙaddamar da wani babban hari a jihar Borno.

'Yan ta'addan sun kai harin ne a hedikwatar runduna ta 29 (29 Task Force Brigade) da ke Benisheikh, a karamar hukumar Kaga ta jihar Borno.

Sojojin Najeriya sun rasa ransu a hannun 'yan ta'adda
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An tabbatar da kisan ne a cikin wata sanarwa da darakta a sashen yaɗa labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Michael Onoja ya fitar a shafin X a ranar Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga saman babura 50 sun yi ta'asa a Zamfara, an kashe jami'an tsaro

An tabbatar da harin 'yan ta'adda kan sojoji

Manjo Janar Michael Onoja ya bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare a ranar 9 ga Afrilu, 2026, lokacin da maharan suka yi ƙoƙarin kutsa kai cikin katangar tsaro ta sansanin sojojin.

Ya ce dakarun rundunar Operation Hadin Kai ƙarƙashin jagorancin kwamandan birged ɗin, sun mayar da martani da kan harin 'yan ta'addan.

“A ci gaba da ƙoƙarin dakarun tsaron Najeriya na yaƙi da ta’addanci, dakarun birged ta 29 a ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun fuskanci wani harin ta’addanci da aka tsara a inda suke a hedikwatar birged da ke Benisheikh, jihar Borno."
“Sai dai dakarun, ƙarƙashin jagorancin kwamandan birged ta 29, Birgediya Janar Oseni Braimah, sun mayar da martani da gagarumar kwarewa, da kuma ƙarfin makami."
"A cikin wani martani da aka tsara cikin basira, an fatattaki ’yan ta’addan tare da tilasta musu tserewa cikin rudani, inda suka bar manufarsu."

- Manjo Janar Michael Onoja

Kara karanta wannan

'Ba haka muka so ba," A karon farko, Isra'ila ta yi nadama bayan kai hari Iran

Meyasa 'yan ta'adda ke farmakar sojoji

Hedikwatar Tsaron ta bayyana harin a matsayin alamar fitar da rai daga ɓangaren ’yan ta'adda, waɗanda suka tafka asara mai yawa a ayyukan sojoji na kwanan nan.

“Wannan hari nuni ne karara na fidda rai daga ɓangaren ’yan ta’adda, waɗanda bayan sun sha kaye sosai a ayyukanmu na kwanan nan, suka ci gaba da neman mafaka ta hanyar kai hare-hare marasa galihu kan sansanonin sojoji masu tsaro sosai."

- Manjo Janar Michael Onoja

Me aka ce kan kisan Janar?

Sojojin sun amince cewa gumurzun ya yi sanadiyyar asarar rayuka a tsakanin dakarunsu, sai dai ba su tabbatar ko su ƙaryata rahotannin da ke cewa Kwamandan Birged ta 29, Birgediya Janar Oseni Braimah, yana cikin waɗanda suka rasa rayukansu ba.

“Abin takaici, fafatawar ta yi sanadiyyar rashin wasu jaruman sojoji kalilan waɗanda suka riga mu gidan gaskiya yayin gudanar da aikinsu."
"Babban hafsan hafsoshi yana girmama jarumtakarsu, sadaukarwarsu, da kuma kyakkyawar aniyarsu ta kare ƙasa."

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutane 20 da ake zargi da hannu a ayyukan ta'addanci a Najeriya

- Manjo Janar Michael Onoja

'Yan bindiga sun kashe sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun farmaki tawagar jami'an sojoji da 'yan sanda a jihar Kebbi.

Mummunan harin kwanton baunan da 'yan bindiga suka kaddamar ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji tara da ɗan sanda ɗaya a ƙaramar hukumar Shanga dake jihar Kebbi.

Rahotanni daga majiyoyi daban-daban sun nuna cewa jami'an tsaron sun fada tarkon ‘yan bindigar ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani kamfanin gine-gine.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng